Shirin Labarina da wasiƙar Zallawa!

Spread the love

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Ga wanda bai san su waye Zallawa ba to a gurguje gungun mutane ne da ke da’awar kafa ƙungiyar zallar Hausawa. Ba wani ma’auni da ke tabbatar da mutanen Hausawa ku kuwa akasin hakan. Haƙiƙa babban abin da akasarin ‘yan wannan gungun su ka shahara a kai shi ne ayyana dukkan Fulani a matsayin ‘yan ta’adda, kushe jihadin Shehu Usmanu Danfodio da nuna jidali ne maimakon jihadi har ma da yayata cewa Sir Ahmadu Bello Sardauna shi ya ja wa kansa fushin su Chukwuma Nzeogwu da su ka yi ma sa kisan gilla. An sha jan hankalin gungun da hatsarin aikinsu ka iya kawo babbar fitinar ɗauki ba daɗi a doron kabilanci musamman tsakanin Musulmi Hausawa da Fulani a Arewa. Gungun kan yi watsi da jan hankalin da amfani da kausasan kalamai da ma kai wag a zayyana duk Fulani a matsayin wadanda a ka haifa ta hanyar zina.

Ashe masu iƙirarin zalla sun naɗa kan su a muƙamin magana da yawun Hausawa ne? Na ga sun ba da wa’adin mako biyu ga hukuma a gwamnatin Kano ta biya mu su buƙata kan fim ɗin LABARINA ko su garzaya kotu.

Da farko dai na sha bayyana mu ku a hukumance ba wata ƙungiya mai rejista da sunan HAUSA ZALLA amma akwai GIDAUNIYAR HAUSAWA da hukumar kula da yi wa kamfanoni rejista CORPORATE AFFAIRS COMMISSION ta yi wa rejista a 2022. Hukuma ta yi wa GIDAUNIYA rejista ne don ba da tallafi ga ‘yan gudun hijira da sauran su amma ba wai a matsayin kungiyar ƙabila ko ma mai magana a madadin Hausawa ba. Duk sahihin Bahaushe na da hurumin takawa masu wannan iƙirari birki da nuna sam ba su da hurumin magana a madadinsa da ma wai kare muradunsa ko ma daukar wannan loga ta yin barazana ga hukumar gwamnatin jihar Kano ta tace fina-finai.

Wallahi ban ɗauka farafagandar nan ta kai wannan mizani da a Kano za a samu wasu da sunan wai Hausawa ne da za su ba wa hukuma wa’adi ta canja wasu sassan fim din LABARINA ko su garzaya kotu. Duk da lauyan da ya yi rubutun daga Funtua ya nuna adireshinsa ya ke, da ba za mu yi mamaki ba idan wasu ‘yan kasa a Kano ba da suna ko fakewa da kabila ba, sun buƙaci biya mu su bukata.

Wani abin takaici ma shi ne yadda Zallawa da ke cewa su na da Musulmi, Kirista da ma masu addinin gargajiya amma a wannan barazana da su ka yi sun kore mabiya addinin Kirista da ‘yan gargajiya daga tafiyarsu, yanzu sun zama wai masu kare Musulmi. Korafin na nuna an gwada Hausawa a fim ɗin da har ma shan giya da hakan a tsarin Zallawa ai ba haramun ba ne tun da su kan ce KABILA JINI CE ADDINI KUMA ZABI NE. Na ga wani ya rubuta wai an kawo batun MAGUZAWA alhali ya manta hatta jagoran wannan tafiya ya zayyana kansa da zama JIKAN MAGUZAWA har ma da alfahari da hakan ta hanyar rubuta Kalmar Shahada cike da kuskure don ƙoƙarin nuna ko da a na ganinsa a matsayin wanda ba Musulmi to yanzu ya musulunta.

Akwai wata kalma da ina ganin CLIENTS ne a takardar barazanar da lauyan ko lauyoyin su ka fassara da ABOKAN CINIKINMU! In haka ne duk da ban ga rubutun turancin ba, ko da AI ne a ka yi fassarar ko Bagware ne ya fassara.

BUƙATAR GA GWAMNATI, HAUSAWAN GASKIYA DA MANYAN ‘YAN FIM

1. Mu na kira ga gwamnatin Kano da ta taka birki ga duk mai iƙirari ko wata barazana da sunan ƙabilanci a Kano don ba inda a tsarin mulki a ka ba wa wani hurumin yi wa gwamnati barazana da sunan ƙabila ko ƙabilanci.

2. Hausawan gaskiya su fito su ƙalubalanci duk wani mai shigar burtu da ba wanda ya naɗa shi don magana a madadinsu har ma a birni irin Kano.

3. Manyan masu harkar fim kama daga shi kansa Aminu Saira da manya na farko irin su Basarake Malam Ibrahim Mandawari, Marubuci Ado Ahmad Gidan Dabino, Alhaji Hamisu Iyan Tama, mawallafin MUJALLAR FIM Ibrahim Sheme, Malam Nasiru Gwangwazo, darakta Ishaƙ Sidi Ishaƙ da sauran su, su ɗau matakin gaggawa kan waɗannan mutanen da ke buɗe ƙofar zagin mutane har ma da bugin kirjin wai za su kai ƙara kotu a madadin Hausawa. Shin dama ‘yan KANNYWOOD Hausawa su ke yaka?.

Na ga wasu akasari masu sunan karya kuma ba hoto ba adireshi na bugun kirjin ɗaukar mataki ko ma ta kai ga sai wanda su ka ba wa lasisi ne zai yi amfani da harshen Hausa! Iyye samun waje ko arahar gabar da kansa ‘yar gagara sallar asuba.

Ga Zallawa maimakon rubuta takardar wa’adi ko gargaɗi, ai kawai su garzaya kotun. Ni yadda na ke ganin surutansu na dauka za su tafi kotun ne don shari’a da gwamnatin Kano. A takardar da na gani, na ga sun yi wa kwamishinan labaru na Kano kofi amma ban ga sunan kwamishinan shari’a ba. Kowa na da hurumin ya buƙaci lauya ya rubuta ma sa takarda amma tambayar- shin akwai lauyan HAUSAWA MAI BARAZANA GA HAUSAWA A KANO DAGA FUNTUA?.

Idan mun duba ɓangaren tattara dukkan Fulani makiyaya a matsayin masu hannu a aikin ta’addanci, hakika hakan rashin adalci ne don wannan fitina da Zallawa ke cewa ta na shafar Hausawa ne kaɗai ba haka ba ne sam. Miyagun iri kan yi dirar mikiya kan kowa kuma a na samun su a kowace ƙabila. Don haka haifar da baraka a tsakanin al’ummar Hausawa da Fulani da ke zaune tare shekaru aru-aru wani makirci ne da maƙiya Arewa da Musulunci ke ingizawa.

Masu yayata farafagandar Zallawa da ya ke Gwarawa ne ba su damu da tantance wadanda ‘yan ta’aadda ke ɗaukewa don karɓar kundin fansa ba. Wallahi ba batun ware wane ƙabila kaza ne ko kaza kawai kuɗi su ke nema. A nan na kawo mu ku yadda su ka ɗauke Sarkin Fulanin Bungudu a jihar Zamfara da Bappayo Samnaja Maudo da sai da a ka biyawa kowanne Naira miliyan 50 kafin a sako su bayan kwana 33.

Bambancin ɗauke matafiya a hanya da kan zama kan mai uwa da wabi da na makiyaya shi ne, yayin da a kan tuntuɓi ‘yan uwan matafiya da a ka sace su kawo fansa, su makiyaya da zarar miyagu sun gamu da su a daji su kan buɗe mu su wuta su yi awun gaba da shanun kuma dillalai ne a cikin gari kan sayi shanun daga miyagun irin. Yo dama dukiya ’yan bindiga ke nema to ga garken shanu ai ba abun jira illa a tura mai shanun lahira a yi awun gaba da dukiyarsa.

Wallahi ina da bayanan makiyaya da ke cikin halin gaba ƙura baya siyaki don in jami’ai su ka gan su ba lallai su yi bincike su tsira ba, haka ‘yan bindiga ma su ke d!rar mu su da sara da suka don dukiyar da su ke yawo da ita da su ka gada daga kaka da kakanni. Shekarun baya a jihar Kaduna ai an ga wasu makiyaya na bin sawun waɗanda su ka ɗauke mu su shanu sai jami’ai su ka cafke su, su ka yi ta loda su daya kan daya cikin mota ina ganin HILUɗ ce. ƙarshe haka su ka yi ta mutuwa kuma daga bisani a ka gano ba su da laifi wai sai jami’an su ka ba da haƙuri.

Wani batun an yi wa wani laifi ko ba a yiwa wani laifi ba, ba wannan magana ce gaskiya ba. Har gobe waɗanda a ke zalunta ba a daina ba inda su kuma masu aikata miyagun laifuka akwai kowa a ciki da baki da fari da ja da kore. Duk mai hawa soshiyal midiya ya cusa ƙabilanci ko wani makirci to tabbas ɗan kwangila ne makiyin al’ummar Arewa.

KAMMALAWA

A ‘yan kwanakin nan mu na ganin yadda sunayen ‘yan IPOB ke fitowa karara su na ingiza farafagandar Zallawa maimakon ma su ɓoye sunayen don kar a gane hannunsu dumu-dumu a kwaryar furar basaja. Hakanan uban Zallawa daga Kamaru Ouba Ali Mohaman da kai da fata ke yaƙi da ‘yan awaren Ambazonia na Kamaru, amma sam ba damuwarsa ba ce in Nijeriya ta kama da wuta ta yadda ya kan ingiza matasa su yi tsegeranci ga dattawan Arewa har ma kan Shehu Mujaddadi.

Tabbas za a samu bayanai masu yawa in an gayyato Ouba ya amsa tambayoyin yadda ya na Kamaru amma ya zaɓi jefo harshen ashana cikin Nujeriya. Ba za a yi sako-sako ba don ai Maitats!ne ma daga yankinsa ya shigo.

Ouba da ke magana da garma-garmar Hausa, amma ya dage wai Zallawa ‘yanci su ke nema! Wane laifi a ka yi mu su? Wa ya taka mu su birki daga cin zarafin masu mutunci da murde wuyan tarihi da su ke yi? Kai wa ma ya san su balle ma har a take mu su haƙƙi ko ‘yanci? Iyye kwangilar wargaza Arewa. Na tabbata mutanen nan ba sa jin daɗin nasarar da a ke samu ta m+rkushe ‘yan ta’addan nan don ta nan su ke fakewa wajen fitar da hayaƙi inda ba murhu, da tsere-tsere har su na tuntuɓe wajen yayata sabon bidiyon ‘yan ta’adda.

Ouba har lambobin girma ya ke ba wa matasa masu ruruta fitinar ƙabilanci da rigar Hausawa a Arewa. Na yi nazarin wasu hotunan da a kan nuna shi da wasu, na ajiye su a gefe don akwai ƙamshin manhajar ARTFICIAL INTELLIGENCE don batar da sawu.

Allah ya sakawa Shehu Mujaddadi da alheri don ya feshe Arewa da addu’a da kan tona makircin duk masu kulle-kulle a bayyane ko a ɓoye da sunan gaskiya ko da na karya da hoton haƙiƙa ko manhajar AI.

By ukarofi

Leave a Reply