Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Ministan yaɗa labarai da wayar da kan jamaʼa, Alhaji Mohammed Idris, ne ya bayyana hakan yayin taron Arewa Media Summit da ofishin mai taimaka wa shugaban ƙasa kan yaɗa labarai da wayar da kai, Malam Abdulaziz Abdulaziz, ya shirya a ranar Litinin a birnin Kano.
Ministan ya bayyana cewa kafafen yaɗa labarai na da muhimmiyar rawa wajen ƙarfafa haɗin kai, juriya da kyakkyawan fata a tsakanin al’umma.
Ya kuma yi gargaɗin cewa yaɗuwar labaran ƙarya da bayanan da ba su da tushe a kafafen sadarwa na iya yin barazana ga haɗin kan ƙasa da amincewar jama’a.
Blueprint Manhaja ta ruwaito cewa a jawabinsa, Malam Abdulaziz Abdulaziz na cewa an shirya taron ne domin ƙarfafa tattaunawa tsakanin gwamnati, al’umma da kafafen yaɗa labarai.
Ya kuma buƙaci masu amfani da kafafen sada zumunta su tabbatar da sahihancin bayanai kafin wallafawa, musamman gabanin zaɓen 2027.
Haka kuma ya bayyana cewa an horas da masu yaɗa labaran APC sama da 100 kafin taron, tare da ƙaddamar da shirin Gani Ya Kori domin nuna manyan ayyukan ci gaba da gwamnatin tarayya da gwamnonin Arewa suka aiwatar.
Da yake buɗe taron Gwamnan Kano, Engr. Abba Kabir Yusuf, ya buƙaci sauran jihohi su kwaikwayi shirinsa na samar da masu ɗauko masa rahoto wato SSR da SR, wanda ya tura matasa sama da 150 zuwa ma’aikatu, hukumomi da ƙananan hukumomi domin inganta yaɗa bayanan gwamnati da wayar da kan jama’a.
Taron ya samu halartar ƴan jarida, masu gabatar da shirye-shirye, masu shirya fina-finai, masu ƙirƙirar ta kafar sadarwa masana, masu tsara manufofi, da ƙwararrun masana harkokin sadarwa, da suka fito daga sassa daban-daban na Arewacin Nijeriya, taken taron na bana shi ne “Gwamnati da ƴan ƙasa: ɗaukar nauyin samar da ɗa’a a aikin ƴaɗa labarai.”
