
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ƙungiyar Mashawartan Arewa na Matasa AYCF, ta nesanta kanta daga saƙon da aka wallafa da ke zargin ta fitar da wata sanarwa mai ƙunshe da goyon ga Shugaban ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila akan al’amarin hukumar bogi ta PFIPC.
A wata sanarwa da ke ɗauke da sanya hannun Shugabanta, Alhaji Yerima Shettima a ranar Lahadi, AYCF ta musanta hannu a fitar da kowane saƙo akan al’amarin.
A cewar sanarwar, wasiƙar da ake yaɗawa ba daga AYCF yake ba don haka al’umma su ƙaurace mata tare da saƙon da ke ciki.
Sanarwar ta bayyana cewa, AYCF ƙungiya ce mai kima da darajar tunkarar dukkan wasu al’amura da suka shafi ƙasa cikin tsanake, ware kai da kuma ƙoƙarin tabbatar da haƙiƙanin al’amari kafin tsoma baki.
Don haka ne ta ce ta fara gudanar da bincike mai zurfi don gano dukkan waɗanda suke da hannu a ciki, manufarsu da kuma masu agaza musu domin ɗaukar matakan da suka dace akansu.
