Shugaban ƙaramar hukumar Augie ya jajenta wa Fulani bisa kisan Alhaji Kiruwa

Spread the love

Shugaban ƙaramar hukumar Augie Honarabul Yahaya Muhammed Augie ya jajanta wa Fulanin Gaɗawande bisa ga kisan gilla da aka yi wa Alhaji Kiruwa Amadu, ɗaya daga cikin shugabannin Fulanin ƙaramar hukumar Augie.

Ya bayyana kisan Kiruwa da waɗansu da a ke sa ran mayaƙan lakurawa ne a matsayin koma-baya a cikin yankin idan aka yi la’akari da irin gudummawar da ya ke bayarwa wajen wanzar da zaman lafiya musamman tsakanin manoma da makiyaya.
Ya bai wa iyalan marigayin haƙuri tare da ba su tabbacin ƙaramar hukumar Augie da gwamantin jiha suna ƙoƙarin yaƙar ta’addanci ba dare ba rana.

Ya yi kira ga Fulanin da su kai rahotannin duk wani baƙo da ba su yarda da shi ba ga hukumomin da ya dace da ke mafi kusa da su a duk lokacin da hakan ta taso wanda yin haka yana taimakawa ƙwarai wajen hana sakewar ƴan ta’adda da kuma ɓata-gari.

By ukarofi

Leave a Reply