Shugaban NSUBEB ya kira al’umma su riƙa kula da kayan makarantun gwamnati

Spread the love

Daga JOHN D WADA a Lafiya

Shugaban hukumar ilimin bai ɗaya ta jihar Nasarawa wato NSUBEB Dr. Kasim Mohammed Kasim ya yi kira na musamman ga al’umma a faɗin jihar baki ɗaya su ɗauki alhakin mallakar makarantu musamman na gwamnati da kuma kula dasu yadda ya dace.

Ya bayyana haka ne yayin wata tattaunawa ta musamman da yayi da wasu ‘yan jarida a ofishinsa da ke Lafia fadar gwamnatin jihar kwanan nan.

Dr. Kasim ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta kashe biliyoyin Naira wajen gyara makarantun da rufinsu ya lalace sakamakon amfani da harabar makarantu a matsayin filin wasan kwallon ƙafa da sauran munanan ɗabi’u.

Ya roƙi sakatarorin Ilimi na ƙananan hukumomi 13 dake jihar da su riƙa sa ido akai-akai a makarantun gwamnati domin hana ƙara lalata su.

“Gwamnatin jihar nan ta zuba kuɗaɗe masu yawa wajen gina makarantu da samar da kayan ɗaki da tebur da kujeru ga waɗannan makarantu,” in ji shi.

Shugaban na NSUBEB ya kuma bayyana damuwarsa kan yadda wasu mazauna ƙauyen a ƙaramar hukumar Akwanga suka yi nasarar kwashe cikakkun tebur da kujeru na wata makaranta.

Ya nuna ɓacin ransa kan ƙaruwar yadda wasu ‘yan daba ke lalata makarantun gwamnati a jihar yana mai gargaɗin cewa duk wanda aka kama da hakan zai fuskanci hukuncin gwamnati.

Dr. Kasim ya ƙara da cewa gwamnatin jihar ta haramta amfani da harabar makarantun gwamnati a faɗin ƙananan hukumomi 13 na jihar a matsayin filin horar da ƙwallon ƙafa inda ya kuma bayar da misali da wani makarantar firamare da sakandare ta Dunama dake cikin babban birnin jihar Lafia da sauran makarantun da aka fi lalatawa a jihar.

Shi dai matashin wato shugaban hukumar ta NSUBEB na gwamnatin jihar Dr. Kasim Mohammed Kasim wakilin mu a jihar ya kuma ruwaito cewa tunda gwamnan jihar Injiniya Abdullahi Sule ya naɗa shi muƙamin ne ya himmatu wajen canja fatsalin makarantu a jihar musamman na gwamnati inda al’ummar jihar gaba ɗaya musamman iyayen yara ɗalibai ke cigaba da yaba masa dangane da namijin ƙoƙarin da yake yi a fannin daukaka fannin Ilimin zuwa matakin cigaba kawo yanzu.

By ukarofi