
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A daiadai lokacin da ‘yan Nijeriya ke cigaba da tsokaci akan badaƙalar hukumar bogi ta PFIPC, Ofishin Akanta Janar na Ƙasa (OACF) ya ce hukumar ba ta da asusun aiki a Babban Bankin Nijeriya (CBN), don haka ba a taɓa tura mata ko sisi daga kuɗaɗen gwamnati ba.
Daraktan hulɗa da jama’a na ofishin a wata sanarwa, Bawa Mokwa, ya bayana cewa an dai fara yunƙurin buɗe asusun ne, amma ba a kai ga kammala shi ba saboda ba a cika wasu sharuɗɗa da ake buƙata ba.
Ya ƙara da cewa, Adeniyi Adeyemi ya gabatar da takardar naɗi lokacin neman buɗe asusun, amma ba a miƙa sunayen masu sanya hannu kan asusun ba, abin da ya hana asusun fara aiki.
Bawa Mokwa ya ce, duk da cewa hukumar bogin tana da kaso acikin kasafi, wani hukunci daga cikin dokokin kasafi bai bayar da damar fitar da kuɗaɗen kai-tsaye ba.
Haka kuma, OAGF ta yi watsi da batun cewa an biya albashi ga jami’an hukumar daga cikin kuɗaɗen gwamnati.
A cewar Mokwa, ba yadda za a yi hukumomin tarayya su ɗibi ma’aikata ba tare da sahalewar Hukumar kula da Ɗa’ar Ma’aikata ta Tarayya, Ofishin Kasafi da kuma Ma’aikatar Ma’aikatun Tarayya ba, kana daga bisani a ɗora su a tsarin biyan albashi na IPPIS.
