
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ɗan wasa Mikel Merino da aka sako daga baya ya yi nasarar zura ƙwallo a raga ana gab da kammala wasa inda aka tashi Sifaniya ta doke Portugal ta su Cristiano Ronaldo da ci 1 da 0 a gasar Kofin Duniya da ke cigaba da gudana a Nahiyar Amurka.
Wannan al’amari ya kawo ƙarshen fatan zakaran ɗan ƙwallon duniya, Ronaldo zuwa ƙarshe bayan gumurzu da ƙasarsa a gasar har sau shida a tarihinsa.
Haka kuma nasarar da Sifaniya ta samu dama ce ta cigaba da aiki tuƙuru wajen ganin ta lashe kofin a matsayinta na ɗaya daga cikin ƙasashen da ake sa ran ka iya ɗaukar kofi.
A ‘yan kwanakin nan ne dai Ronaldo mai shekaru 41 ya bayyana cewa wannan shi ne karo na ƙarshe da zai kasance acikin gasar Kofin Duniya na FIFA a matsayin na ɗan ƙwallon ƙafa.
Tuni dai ƙasashen Faransa, Norway da Moroko suka samu tikitin shiga zagayen wasannin dab da na kusa da na ƙarshe kamar Sifaniyar.
