Daga JOHN D WADA a Lafia
Shugaban jam’iyyar adawa ta NDC na ƙasa reshen jihar Nasarawa Hon. Dogo Shammah ya ce jam’iyyar tamkar jirgin Annabi Nuhu ne dake shirye ya ɗauki duk wanda ke son cigaba da ingantaccen rayuwa da kuma ainihin shugabanci nagari a jihar da ƙasa baki ɗaya.
Hon. Dogo Shammah ya bayyana haka ne a lokacin da yake tattaunawa da wakilin mu a gidan sa dake Lafia babban birnin jihar.
Yace ba shakka jam’iyyar ta NDC a yanzu tana cigaba da samun karɓuwa na musamman a jihar ta Nasarawa da ƙasa gaba ɗaya da hakan yasa jam’iyya mai mulki a jihar wato APC ma ke tsoron ta, shi yasa suke ta yin duk mai yuwa don tabbatar sun kawo mata cikas amma ba za su yi nasara ba.
Yace jam’iyyar ce kaɗai cikin duka sauran jam’iyyun adawa za ta iya ƙwace ragamar mulki daga APC ta kuma cire wa ‘yan Najeriya kitse a wuta.
Shugaban NDC a jihar Hon. Dogo Shammah ya kuma yi amfani da damar inda yayi Allah-wadai da matakin da hukumar shirya zaɓe INEC ta ɗauka na hana jam’iyyar fafatawa a zaɓen cike gurbi na shiyar sanatan Arewacin jihar da aka kammala kwanan nan, wato ta ƙi saka tambarin jam’iyyar a katin kaɗa ƙuri’a kamar yadda tayi wa sauran jam’iyyun da gangan tare da hukuncin nan na wani kotun tarayya da ke ƙoƙarin hana su karawa a zaɓukan 2027 a jihar da ƙasa baki ɗaya inda yace tabbas dole ne su ƙalubalanci matakin na INEC da kotun a kotuna na gaba.
Ya kuma yi amfani da damar inda yayi kira na musamman ga al’ummar jihar gaba ɗaya su fito ƙwansu da kwarkwata su yi rajista a sabuwar jam’iyyar ta NDC su kuma tabbatar sun samu katin kaɗa ƙuri’ar su don basu damar ƙwato mulki daga wajen APC wadda ya bayyana a matsayin muguwar uwa dake kashe ‘ya’yan ta.
A ƙarshe sai Hon. Dogo Shammah ya sanar cewa a halin yanzu tuni jam’iyyar ta kammala duka zaɓukan gwanayen ‘yan takaran ta a duka matakai cikin lumana da gaskiya inda ta kuma kafa wani kwamitin sulhu da zai sasanta duk wani saɓani da ka iya aukuwa bayan an sanar da waɗannan sakamokon a hukumance kana ya bayyana cewa duka waɗanda aka zaɓan don riƙe tutar jam’iyyar a zaɓen gama gari na 2027 dake tafe mutane ne masu mutunci da kima gun al’umma, sa’anan yace tabbas za su yi nasara a zaɓukan insha Allah.
Wakilin namu a jihar ta Nasarawa ya kuma ruwaito cewa a kwanakin baya ne dai jam’iyyar ta NDC mai tambarin yatsu biyu ta nada shi Hon. Dogo Shammah wanda tsohon kwamishinan yaɗa labarai da raya al’adun gargajiyan jihar ne a matsayin shugaban jam’iyyar a jihar.
