Fitilar bada hannu: Ma’ana, muhimmancinta da illar rashin amfani da ita

Spread the love

Tare da BILKISU YUSUF ALI

Gabatarwa

A zamanin yau, harkokin sufuri da zirga-zirgar ababen hawa sun zama wani muhimmin ɓangare na rayuwar ɗan adam, musamman a birane. Yawaitar motoci da  babura da masu tafiya a ƙafa ya haifar da buƙatar tsari mai kyau domin tabbatar da tsaro da ingantacciyar zirga-zirga. ɗaya daga cikin manyan hanyoyin da ake amfani da su wajen sarrafa zirga-zirga shine fitilar bada hannu, wato traffic light a turance.

Fitilar bada hannu wata na’ura ce da ake sanyawa a hanyoyi domin sarrafa motsin ababen hawa da masu tafiya a kafa ta hanyar amfani da launuka uku: ja, rawaya da kore. Wannan takarda za ta yi bayani kan ma’anar traffic light, muhimmancinta a cikin al’umma, da kuma illolin da ke tattare da rashin amfani da ita.

Ma’anar fitilar bada hannu:

Traffic light (fitilar zirga-zirga) wata na’ura ce da ake sanyawa a mahadar hanyoyi domin ba da umarni ga direbobi da masu tafiya a kafa. Wannan na’ura tana amfani da launuka uku:

Ja (Red): Tsaya

Rawaya (Yellow/Amber): Shirya tsayawa ko fara tafiya

Kore (Green): Tafi

A cewar (Adebayo, 2018), traffic light wata hanya ce ta zamani da ke taimakawa wajen rage hadurra da tabbatar da tsari a hanyoyi. Haka kuma (World Road Safety Report, 2020) ya bayyana cewa traffic light na daga cikin muhimman kayayyakin kula da tsaro a hanyoyi.

Tarihin Samuwar Traffic Light

An fara amfani da traffic light a shekarar 1868 a birnin London, inda aka fara amfani da ita domin sarrafa zirga-zirga. Daga baya aka inganta ta zuwa wacce ke amfani da lantarki a shekarar 1914 a Amurka.

A yau, traffic light ta zama ruwan dare a duniya baki daya, musamman a manyan birane kamar Lagos, Abuja da Kano.

Muhimmancin fitilar bada hannu:

1. Rage haɗurra

Fitilar bada hannu na taimakawa wajen rage hadurra a hanyoyi ta hanyar tsara motsin motoci. Lokacin da kowa ya bi dokar fitila, hadurra suna raguwa sosai.

2. Kula da tsari a hanya

Fitilar zirga-zirga na tabbatar da cewa kowane bangare na hanya yana samun dama cikin tsari. Wannan yana hana rikice-rikice a mahadar hanyoyi.

3. Kare rayukan jama’a

Masu tafiya a kafa suna samun kariya ta hanyar traffic light, musamman a wuraren da aka ware musu hanya (pedestrian crossing).

4. Rage cunkoso

Traffic light na taimakawa wajen rage cunkoso ta hanyar tsara yadda motoci ke motsi a lokaci daban-daban.

5. Inganta gudanar da sufuri

A cewar (Ogunleye, 2019), amfani da traffic light na kara ingancin harkokin sufuri da rage bata lokaci.

Illolin rashin amfani da traffic light:

1. Yawaitar haɗurra

Rashin bin dokar traffic light na haifar da hadurra masu yawa, wanda ke janyo asarar rayuka da dukiya.

2. Rikice-rikice a hanya

Lokacin da direbobi ba su mutunta traffic light ba, ana samun cacar baki da rikici a hanyoyi.

3. Cunkoso mai tsanani

Rashin amfani da traffic light na jawo cunkoso mai tsanani, musamman a manyan birane.

4. Asarar lokaci

Direbobi da fasinjoji suna bata lokaci mai yawa saboda rashin tsari a zirga-zirga.

5. Lalacewar doka da tarbiyya

Rashin bin traffic light na nuna rashin biyayya ga doka, wanda ke lalata tsarin zamantakewa.

ƙalubalen amfani da fitilar bada hannu a Nijeriya:

A Najeriya, akwai wasu matsaloli da ke hana amfani da traffic light yadda ya kamata:

Rashin wutar lantarki

Lalacewar na’urorin

Rashin wayar da kai

Rashin bin doka daga direbobi

A cewar (FRSC Report, 2021), yawancin hadurran mota a Najeriya na faruwa ne saboda rashin bin dokokin zirga-zirga, ciki har da traffic light.

Hanyoyin magance matsalolin:

1. Wayar da kai

Ya kamata gwamnati da kungiyoyi su wayar da kan jama’a muhimmancin bin traffic light.

2. Gyaran na’urori

A tabbatar da cewa dukkan traffic light suna aiki yadda ya kamata.

3. Hukunta masu laifi

Dole ne a dauki matakin hukunta masu karya dokar traffic light.

4. Samar da wutar lantarki

A samar da hanyoyin samar da wutar lantarki mai dorewa domin aiki na’urar.

Kammalawa:

Fitilar bada hannu wata muhimmiyar hanya ce ta kula da zirga-zirga a duniya. Tana taimakawa wajen rage hadurra, kare rayuka, da inganta tsarin sufuri. Duk da haka, rashin amfani da ita na haifar da matsaloli masu yawa kamar hadurra, cunkoso da asarar rayuka.

Don haka, yana da muhimmanci kowa ya kiyaye dokokin traffic light domin tabbatar da tsaro da zaman lafiya a hanyoyi.

Manazarta (References)

Adebayo, A. (2018). Road Traffic Management in Nigeria. Lagos: Spectrum Books.

Federal Road Safety Corps (FRSC) (2021). Annual Road Safety Report. Abuja.

Ogunleye, T. (2019). Urban Transportation Systems. Ibadan: University Press.

World Health Organization (2020). Global Road Safety Report. Geneva.

Yusuf, M. (2022). Hanyoyin Kula da Tsaro a Najeriya. Kano: Gidan Dabino Publishers.

By ukarofi

Leave a Reply