Switzerland ta kai kwata fainal bayan doke Kolombiya a fenareti

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Yayin da ake cigaba da fafatawa a gasar Kofin Duniya na 2026, Ƙasar Switzerland ta yi nasarar kaiwa zagayen wasannin dab da na kusa da na ƙarshe bayan doke Kolombiya da ci 4 da 3 a bugun fenareti a zagayen ‘yan 16.

Da fari, an tashi wasan ne babu ci a tsakanin ɓangarorin biyu bayan shafe mintina 120 ana gumurzu a wasan mai cike da ɗaukar hankali.

Luis Díaz na Bayern Munich ne kaɗai ya zubar wa Kolombiya fenareti, lamarin da ya ba Switzerland nasara a wasan.

A yanzu, ƙasar za ta kara da Argentinar su Lionel Messi da ta doke Misra da ci 3 da 2 biyu bayan farfaɗowa daga ƙwallo biyu da aka zura mata a wasansu na ranar Talata.

Ga jerin haɗin ƙasashe takwas da suka rage a gasar da ke gudana a Nahiyar Amurka a hoton da ke ƙasa:

By Babaji