07
Aug
A makon jiya, Nijeriya ta yi rashin ɗaya daga cikin fitattun jami'an gwamnati da suka yi wa ƙasa hidima cikin gaskiya da riƙon amana, wato Alhaji Abubakar Alhaji (Sardaunan Sakkwato). Rasuwar wannan dattijo ɗan kishin ƙasa, tsohon Ministan Kuɗi, kuma tsohon Jakaden Nijeriya a Birtaniya, bankwana ce da wani mutum wanda rayuwar sa ta kasance abar koyi ta ladabi, kishin ƙasa, tawali'u da sadaukar da kai wajen bautar ƙasa. Alhaji Abubakar Alhaji ya rasu bayan ya shafe makonni yana fama da rashin lafiya. Da farko an kwantar da shi a Asibitin Koyarwa na Jami'ar Usmanu ɗanfodiyo da ke Sakkwato, kafin…
