Trump ya jefar da ƙwallon mangwaro

Spread the love

Daga ALI ABUBAKAR SADIQ

To, yau dai 1st ga watan Mayu, 2026 wato bayan kwanaki 60 da shugaba Trump ya biyewa Netanyahu su ka far ma Iran, ya ce yakin da ya yiwa sun “Epic Fury” (Mummunan fushi), ya zo karshe a shari’ance. E, a shari’ance ne saboda dokar Amurka ta yi tanadin cewa shugaban kasa zai iya shiga yaki ba tare da cikakkiyar sahalewar majalisa ba idan ya gamsu da wata barazana ga Amurka. Amma akwai sharadin cewa lallai ne bayan kwanaki sittin ya dawo gaban majalisa ya nemi sahalewar majalisa domin ci gaba da yakin.

A yau gwamnatin ta Trump ta jefar da kwallon mangwaro domin ta san cewa ba za ta iya samun kaso 2/3 na majalisa su sahale mata ci gaba da yakin ba. Sannan kasar Amurka ta tafka asarar da aka kiyasta ta kai dala biliyan $50 wajen kaddamar da yakin. Sannan sakamakon hauhawar farashin mai a Amurka daga dala $2.9 a duk galan na mai kafin a fara yaki, zuwa yanzu ya koma dala $4.1 kan kowane galan. Abinda ya janyo wa Yan kasar asarar kudaden da su ka kai dala biliyan $28 a tsawon watanni biyun nan. Haka Kuma hauhawar farashi ta karu daga kaso 3.8% zuwa 4.7%.

A duk muradun da su ka saka Amurkan ta ce domin ta kai hari a Iran babu guda daya da aka cimma, illa dai asarar rayukan wasu sojojinta, rushewar manya-manya sansanoninta guda 17 a fadin gabas ta tsakiya, asarar jiragen yaki mahimmai kimanin 40 wadanda su ka hada da jiragen yaki, helicopters, drones masu matuka da drones marasa matuka.

Tsakanin Israel, ƙasashen Gulf da jiragen ruwan yakin Amurka, sun karar da makaman kakkabo makamai masu linzami da drones sama da guda 1000, wadanda aka kiyasta kudinsu a dala biliyan $11.

Uwa-Uba shine yadda kafin yakin Mai yana dala $63 amma a yau ya kai dala $125, kuma mashigin Hormuz na bude, a yau ya kasance rufe abinda ke ci gaba da haifar da matsala ga ilahirin tattalin arzikin Duniya.

A karshe dai, duk da asarori na rayuka da dukiya, mu na iya cewa yakin ya kawo karshen fankama da Amurka ke nunawa da zubewar mutuncinta a idon Duniya. Domin a karon farko hatta kasashen Turai sun juya mata baya. Kasashen larabawa munafincinsu ya fito karara sannan sun ji kunya da zubewar mutuncinsu a idon Duniya. Sannan Israila ta kwashi kashinta a hannu domin ta yi asarar rayuka 40 da jikkitattu mutum 8000 banda rushewar gine-gine sama da 28,000. Israila ta kashe dala biliyan $11 wajen asarar kayan yaki da ta yi amfani da su sannan tattalin arzikinta ya janyo asarar dala biliyan $20. Ga kuma mummunar tsana da take ta kara samu daga kasashen Duniya, hatta turawan da a baya ke goyon bayan ta. Duk da cewa Iran ta fi samun asarar rayuka da rushewar gine-gine sakamakon harin bam, mu na iya cewa zai zamar mata gobarar titi a nan gaba, ba kawai a siyasar Duniya ba har da tattalin arziki.

Dan hakin da ka Raina….

Malam Abubakar mai nazarin harkokin yau da kullium ne

By ukarofi

Leave a Reply