17
Jul
Kaddamar da shirin Gani Ya Kori Ji da aka yi a makon jiya wata muhimmiyar hanya ce ta inganta ɗaya daga cikin raunin da aka daɗe ana gani a tsarin yadda ake gudanar da mulki a Nijeriya—wato sadarwa da jama'a. Ana auna gwamnati ba kawai da yawan ayyukan da ta aiwatar ba, har ma da yadda take iya isar da bayanan waɗannan nasarori ga al'umma. A wannan fanni, shirin da Mataimaki na Musamman ga Shugaban ƙasa kan Harkokin Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Abdulaziz Abdulaziz, ya ƙaddamar ya cancanci yabo. Manufar shirin na Gani Ya Kori Ji mai…
