22
Feb
Tare da ABBA ABUBAKAR YAKUBU A wasu shekaru da suka gabata, tashar rediyon BBC ta taɓa gabatar da wata tambaya ta kacici-kacici mai taken, Wane ne yake da tasiri a rayuwarka? Masu sauraro daga sassan duniya daban-daban sun yi ta bayyana tunane-tunanensu, dangane da wanda suke ganin shi ne ya fi tasiri a rayuwarsu. Wani mai sauraro daga wata ƙasar Turai ya bayyana cewa, matarsa ce ta fi komai tasiri a rayuwarsa, sakamakon ita ce ke sarrafa duk wani abu da ya shafe shi. A lokacin na daɗe ina jinjina wannan magana da mamaki a kanta, mai yiwuwa ƙila saboda…