Mahangar duniya tana ga mai ita

Daga SAFIYYA JIBRIL ALIYU

Yayin da malam Bahaushe a azancinsa yake kallon ta a matsayin budurwar wawa, a musulunce kuma sai ake kallon ta a Aljannar kafiri kurkukun mumini.

Shi kuwa Shehin marubucin Ingilishi William Shakespeare sai ya kalle ta kacokan a dandali, fage na kafcen kwaikwayo da kowa yake da ƙofar shiga da ƙofar fita, da kuma rawar da zai taka a tsakar dandalin.

To amma shi ɗan sama-Jannati Carl Sagan ya kalle ta ne kacokan a matsayin shuɗin ɗigo, mahangar da gaba ɗaya ta sa na tsunduma ciki a matsayina na ‘yar Nijeriya. Tafiya nake cike da mamakin duk yawan al’umma ba mu cike wannan ɗigon ba, hasali ma wani ɗan tsukukun waje ne a cikin ɗigon muke a takure, a sakaye.

Mamaki ya ƙara cika ni da na tuna kenan a ɗigon nan ne fa Fir’auna ya ci karensa babu babbaka? Ƙaruna ya yi fankama? Mafi kusa da ni a tarihi, a wannan shuɗin ɗigon ne dai Hitler ya yi tashi fankama da tashin-tashinar? A nan duk wasu ifritai, da salihan cikin Aljannu suke watayawa?

Hakan ya sanya ni son ganin tunƙwal uwar daka a matsugunin Nijeriya cikin shuɗin ɗigon. Nan na ci karo da magada Annabawa sahihai da masu sanya rigar malanta duk don gyara tukwanen miyarsu, ban gama ankarewa da su ba na tsinci rikicin masarauta, ƙani ya yi ma yayansa mai jiran gado kurciya har ya bazama, wai har a rasa ganin sa cikin tsakurin ɗigo, shi kuma ya hau karaga ya harɗe yayin da wani ɗan uban da ke harin kujerar shi ma zai yi silar gushewar hankalinsa!

Yayin da masu ilimin kimiyya da fasaha ke hada-hadar ƙirƙiro ababen da za su ƙawata ɗigon nan a wani ɓangaren wasu na dambarwar aƙida, kowanne na gwada fifikon tsarkinsa. Ga ‘yan siyasa mahandama na ƙoƙarin cika aljihunsu da dukiyoyin da zai nesanta su da haularsu daga raɗaɗin talauci.

Masoya ma ba’a bar su a baya ba, waɗanda romon soyayyar ta yi ƙarko da waɗanda nasu ya riski ajali tun kafin su kai ga dabo-dabo. Majnun da Lailarsa, Romiyo da Juli, har ma su Lantana da Talle duka! A wannan ɗan shuɗin ɗigo ne suka tsinke furensu, suka nutse a ƙoramu, zukatansu suka yi fuffuke suka lula duniyar mafarkai da romansiyya.

Na ci karo ma da mashahurai masu fankama da dukiya da shuhurarsu, ga ƙarfafa jarumai ga malalata, hafsoshin sojinmu har ma da ‘yan fashin daji, haka nan na ci karo da zahidai masu tsantseni ga rayuwa.

Matar mutum ta yi mugunta da makirci duk akan miji, su gallaza ma ‘ya’yan da ba su suka haifa ba duk don biyan buqatun rayuwa. A yi barbaɗe a yi surkulle, a yi binniya da ƙulumboto, a ɗaura guru a ɗaura laya, a rambaɗa kwallin mallaki duka dai a wannan shuɗin ɗigo!

Har ƙafafuna sun sage da tafiya, na fara zaton ko na kai ga gaci sai kuma na iske ƙoramar jini na gudana, waigawar da zan yi ne na hango wani ya jikkitar da mutum zai yanka duk don ya yi kuɗi!

Kai! In duk wannan a shuɗin ɗigon nan ake yi yayin da sauran ƙasashen duk su ma an yanka musu ire-iren wannan a cikin shuɗin ɗigon, ya ƙara tabbatar min da lallai, duniya budurwar wawa ce, kuma, shuɗin ɗigo ce mafi kusa a fahimta da ɗigon ba.

Safiyyah Jibril Abubakar, marubuciya kuma manazarciya a kan al’amurra na yau da kullum. Ta rubuto daga jihar Kaduna.