Darasin haƙuri a zamantakewa (2)

Daga AMINA YUSUF ALI

Barkanku da jimirin karatun Manhaja. A wannan mako mun zo muku da bayani a game da yadda za a gyara aure ta hanyar yin haƙuri a gidan Malam Bahaushe. Amma fa haƙurin ta ɓangaren masu gida, wato maza.

Saboda a zahirin gaskiya, rayuwar auren Bahaushe tana cike da rashin haƙuri da rashin fahimtar juna musamman kum ta fi ƙarfi a ɓangaren maza. Kuma an fi ganin mata ya kamata su yi haƙuri banda maza. A kullum idan aka samu kuskure daga namiji, sai iyaye su tursasa ‘ya’yansu mata su yi haƙuri su zauna da shi, su yi addu’a tare da fatan shiryuwa a gare shi.

Ko da kuwa laifinsa na zina ne, ko dukan mace, ko ƙaurace mata, ko hana ta haƙƙoƙin da Allah ya ɗora masa nata. Shin su ma maza ana yi musu irin wannan nasihar? Idan ya kama matarsa da laifi a ce masa ya je ya cigaba da haƙuri da yi mata fatan ta gyara? Gaskiya hakan yana da matuƙar wahala. Sai dai ma idan ya ba wa iyaye, ko dangi ko abokansa labarin rashin kyautatawar matarsa, sai a dinga bijiro masa da zancen ya rabu da ita. Ya sake ta kenan ko a ce masa ya ƙaro mata, hakan zai sa ita uwargidan ta gyara halayenta?

Dukka waɗannan abubuwa biyu wato saki da ƙaro auro da ake kawowa a matsayin maslaha ga namiji su ne kaɗai maslaha? Kada mu manta fa al’ummar Bahaushe da ma ta yi ƙaurin suna wajen auri-saki da yawan mace-macen aure. Anya ba za mu sauya tunani ba?

Anya tunda dama ta ƙiya ba za mu koma hagu ba? Anya ba za mu dinga sulhu ba mu fahimci juna maimakon kullum ana saki ana ƙaro auren amma ba canji. Kuma ga shi shi wannan savani wajibi ne a cikin dukkan wata alaqa. Tsakanin ‘yanuwa ma ana yi ko abokai. To me ya sai ɓarakar aure ce ita ma ba za a bi ta da allura da zare a ɗinke ta ba?

Misali namiji ya kawo ƙorafin matarsa ga danginsa tana yin wasu abubuwan da bai kamata ba. Sai kawai su ba shi shawarar ko dai ya ƙaro auren ko kuma ya sake ta. Wanda hakan ba ita ce shawarar da ta kamata ba. Me ya sa ba za a zauna a gyara ba? Na ga maza da yawa da suka ƙaro aure ko suka rabu da matansu suka auri wasu. Amma sai matsalolinsu suka ƙara ta’azzara.

Kuma ya afka kogin da na sani. Ba mamaki fa har da rashin ba su shawara mai kyau daga magabata. Sannan wani abun idan ya gagara ai addu’a ake yi. Sai Allah ya shigo lamarinku ya yi gyara.
A addinace ma fa sulhu aka koyar da mu a aure. Musulunci ya samar da matakai na sulhun ma’aurata. Tun daga matakin sulhu a tsakaninsu har zuwa sulhu a tsakanin magabatansu. Sai idan abin ya ci tura ne, kuma rabuwar ta fi alfanu, sai a rabu ɗin.

Ma’aurata ku matso ku ji. Gara ma namiji ya haƙura da wacce yake tare da ita in dai ba wani mugun hali ne da ita ba wanda ka san zai iya gurɓata maka zuri’a. Duk da dai mata da yawa suna da wasu mugayen hali da suke yi domin wahalar da mazaje. Musamman ma idan sun ga su kaɗai ne ba su da kishiyoyi. Su sani idan ba su gyara hali ba, suka tunzura namiji zuwa bangon ƙarshe zai iya rabuwa da su. Idan kuma rabuwa ta afku, sai ka ga dukkan ɓangarorin an afka a kogin nadama. To me ya yi zafi da ido zai ci wuta? To kowa ya gyara mana.

Hanyoyin da za a bi a kiyaye hakan sun haɗa da, idan saɓani ya afku a gidan aure, kawai sai wanda ya san shi ne da laifi ya fito ya amsa laifin ya ba da haƙuri. Ba kuma wai ba da haƙuri kawai ba, a ba da haƙuri da zuciya guda. Ba wai ka ce na san laifina ne amma kaza-da-kaza. A’a ba da haƙuri kawai. Idan macen ce ma haka.

Za mu tsaya a nan sai mako na gaba za mu ci gaba idan rai ya kai. Jinjina da godiya ga masu kira da addu’a da fatan alkhairi. Allah ya ƙara albarkar rayuwa kuma ya biya dukkan muradai.