Daga FATUHU MUSTAFA
Ya kamata dai a yi mana cikakken bayani, shi wannan auren da ake so a ƙulla a jihar Kano, wai bazawara ce ko budurwa, ko ƙwaila ce za a aurar. Wa za a ba, kuma wai ma wa zai aura?
Shin ma an kai kayan mun gani muna so kuwa? Ko an kai kayan banti? Allah ya sa bazawarin ko saurayin yana bayar da kuɗin toshi, ko ɗaurin kaba (in har wacce za a aurar din ta fara ƙirgar dangi).
To amma wane irin aure ne ma za a yi?
A ƙyanƙyara ne (auren zamani), ko auren ɗauki sandarka? Ko kuma dai daduro za a ƙulla (matsalar daduro dai akwai tasau). Ko kuma Kwamaza za a yi, auren Katsinawa? Tunda akwai mabiya shi’a kila ma a ɗaura auren mutu’a, ko a koma vangaren salafiya a yi misyar, to ai duk ana yin su a ƙasar hausa.
Ƙila kuma auren sadaka ne, amma kuma na ga kamar uban ‘yar ba ya so. In kuwa haka ne ka ga ba zai yiwu a yi auren sadaka ba, don ban ga wani abin ku zo ku gani da angon ya tsinana da har za a ɗau ‘ya sukutum da gararta ta tagomashin gwamnatin tarayya a miƙa masa ba.
Shi kuma auren dole ai dai a bari waliyai su amince. Na ga kamar waliyan ba sa ma jituwa, balle ma har a tilastawa ‘yar mutane ta auri wanda ba ta so.
Ga shi kuma ba auren dangi ba ne, domin da alama dai ba gamin danga da garahuni. Kuma na ga alama, zomo ba baran giwa ba ne, zaman dawa ne ya haɗa su.
Koma dai wanne aure ne, mu ‘yan ɗaukar amarya ne, in an ce mu ɗauka, mu ɗauka, in an ce mu sauke, mu sauke.
Faƙat! Dan karuwa ya mutu ranar tarewar ta!
Fatuhu Mustafa ɗan jarida ne kuma mai sharhi a kan lamurran yau da kullum musamman na siyasa. Ya rubuto daga Birnin Tarayya Abuja.
