Annobar cutar aladu ta ɓarke a Jihar Filato – Gwamnatin Filato

Spread the love

Daga HABU ƊAN SARKI, a Jos

Gwamnatin Jihar Filato ta tabbatar da ɓarkewar annobar cutar African Swine Fever, mai saurin kashe aladu, wacce kawo yanzu ta kashe aladu fiye da 5000 daga gonakin kiwon aladu 280.

Gwamnatin ta sanar da haka ne a cikin wata sanarwa da ta fito daga ma’aikatar kula da dabbobi ta Jihar Filato, inda aka bayyana cewa, kawo yanzu cutar ba ta da magani kuma ba ta da rigakafi.

Harwayau, sanarwar ta bayyana takaici kan yadda kimanin wata biyu da fara ganin alamun cutar amma masu gonakin ba su yi gaggawar sanar wa hukumomin abin ya shafa ba sai da cutar ta fara muni sosai.

Ma’aikatar ta tabbatar wa da jama’a cewa, wannan cuta tana illa ne kaɗai ga aladu ban da mutane, kuma ba ta shafar abincin da aka dafa da naman alade. Sai dai ta gargaɗi jama’a su guji yaɗa jita-jita game da cutar ko haɗarin da ake zaton tana yi, don kaucewa yaɗa labaran ƙarya akan cutar.

Kawo yanzu dai jami’an ma’aikatar da ƙwararrun masana lafiyar dabbobi suna nan suna aikin killace gonakin da aka samu bayyanar wannan cuta da yin feshin magani a inda ake zargin an samu alamun cutar. An buƙaci masu harkar kiwon aladu su tabbatar suna kula da tsaftace gonakin su, da biyayya ga ƙa’idojin kiwon dabbobi, da kuma ware aladu masu ciwo da masu lafiya.

By ukarofi

Leave a Reply