“Marubuta ‘yan uwan juna ne, amma kowa da ’yan ɗakinsu”
Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU
Mai karatu barkan mu da sake saduwa a wannan shafi na Adabi a jaridarku ta Manhaja, inda muke kawo muku hirarraki da marubuta da nazari kan ayyukan adabi. A wannan makon mun zaƙulo muku wani matashin marubuci ne ɗan Jihar Kano, wanda tun yana ƙarami ya samu kansa a harkar rubuce-rubuce, tare da tallafin mahaifinsa, har kuma ya zama ɗaya daga cikin masu ba da gagarumar gudunmawa a harkar rubutun adabi ta onlayin. Muhammad Sani Lawal wanda aka fi sani da Sayyid ya shaidawa wakilinmu Abba Abubakar Yakubu cewa burinsa shi ne ya zama fitacce marubuci, kuma hamshaƙin ɗan kasuwa, wanda zai taimaka da basirarsa da dukiyarsa wajen cigaban ƙasa.
MANHAJA: Ina son mu fara da gabatarwa tukunna, wane ne Sayyid Marubuci?
SAYYID: Asalin sunana shi ne Sani Muhammad Lawan, amma an fi sanina da Sayyid ko kuma Legend’s Pen. Ni matashin marubuci ne, sannan kuma ɗalibi mai nazarin harkar kasuwanci. Ina kuma gudanar da sana’ar sayar da kayan waya a kasuwar Titin Beirut da ke Kano. Na kuma koyi sana’ar ɗinki, ita ma ina taɓawa. Ni ɗan kasuwa ne sosai, ina abubuwa da dama na neman halal, don dogaro da kai.
Me ya sa ake ce maka Sayyid?
To, kamar yadda na faɗa a farko, asalin sunana Muhammadu Sani, kuma na ci sunan ƙanin Kakana ne. Shi ya sa ake yi min alkunya, da Sayyid a maimakon kira da Sani kai tsaye. Akasari kamar yadda muka taso muka ga ana yi, a al’adar Bahaushe idan an sa wa yaro sunan kakansa akan yi masa alkunya, ko dai a kira shi da Magaji, Babangida, Abba, Babawo, da sauran su. Yanzu kuma a zamanance akan yi amfani da sunaye irin su Sayyid, Abulbayt ko Abulkhairi da sauran su. Ka ji dalilin kirana da Sayyid kenan.
Ka ba mu tarihin rayuwarka a taƙaice.
An haife ni a ranar 20 ga watan Yuli, a shekarar 2004, a Unguwar Sharaɗa, da ke cikn ƙaramar Hukumar Birnin Kano wato Municipal. Na yi karatun firamare har zuwa sakandire a makarantar Salama da ke nan Sharaɗa NNDC. A halin yanzu, ina cigaba da karatuna na matakin digiri a Jami’ar Northwest Kano, a Sashen Gudanar da Kasuwanci (Department of Business Administration). A ɓangaren addini kuma na yi sauka a shekara 2020.
A rayuwata na mayar hankalina ne kan abubuwa uku, gina ilimi, gina kasuwanci domin dogaro da kai, da kuma amfani da alƙalami wajen isar da saƙonni masu tasiri ga al’umma.
Tun ina ƙarami na taso da sha’awar karance-karance da rubutu. Na fara da karanta gajerun labarai da littattafai kafin na fara gwada rubutu na kaina.
Me za ka iya tunawa a rayuwarka, wanda ya faru da kai tun kana tasowa, da a yanzu sanadin sa rayuwarka ta zama cikin nasara?
Abin da ba zan taɓa mantawa da shi ba tun ina tasowa shi ne, yadda na taso da matsananciyar sha’awar karanta dukkan littafin da ya faɗa hannuna, daga littattafan adabin Hausa har zuwa na ilimin addini da boko. Wannan al’ada ta cusa mini zurfin tunani, saurin fahimtar ɗan’adam, da kuma son neman ilimi ba tare da gajiya ba.
Bugu da ƙari, wani babban al’amari da ya gina matakaina na nasara shi ne sadaukarwa da ƙwarin gwiwar da mahaifina ya riƙa ba ni wajen gyara harshe da amfani da kalmomi masu amfani. Ba kawai ya buɗe mini ƙofar zama marubuci ba, har ma ya koya mini jajircewa da kasancewa mai neman na kai. A yau, wannan halayya ta son karatu da juriya ita ce ginshiƙin da ke riƙe ni wajen tafiyar da karatuna, gudanar da kasuwancina, da kuma rubutu.
Yaya aka yi ka samu kan ka cikin harkar karance-karance da rubutu?
Tafiyata a fagen karance-karance da rubutu ta fara ne tun ina ɗan ƙarami, sanadin matsananciyar sha’awar karanta duk wani rubutu da ya faɗa hannuna. A wancan lokacin, duk sanda na samu littafi ina karanta shi cike da farin ciki da nishaɗi.
Sannu a hankali, wannan tsananin karatu ya fara juyawa zuwa samun ƙwarin gwiwar sanya nawa tunanin a faifai. Maimakon in tsaya a matsayin mai karatu kawai, sai na fara jarraba ƙirƙirar gajerun labarai da ke yawo a kaina. Haɗawa da albarkar shawarwari daga mahaifina wajen faɗaɗa amfani da kalmomin Hausa, gami da shigata ƙungiyoyin marubuta, sun ƙara gogar da ni har na gina kaina a matsayin marubuci a yau.
Wanne rubutu ka fara yi a rayuwar ka a matsayin littafi ko gajeren labari, wanda ya fara buɗe maka ƙofa a harkar rubutun adabi? Kuma akan me ka yi rubutun?
Littafin da na fara rubutawa wanda ya zama tsani kuma ya buɗe mini ƙofa a harkar adabi shi ne. ‘Tudu A Kwari’. Littafi ne da ya binciki yadda soyayya ke fuskantar ƙalubale na zamani da halayyar ɗan Adam, tare da nuna yadda haƙuri da juriya ke mayar da sharri ya koma alheri, kamar dai yadda sunan littafin yake nuni da cewa rayuwa kanta cike take da hawa da sauka (tudu da kwari). Shi wannan littafi shi ne ginshiƙin da ya fito da sunana ya kuma ba ni ƙwarin gwiwar cigaba da gudanar da sauran rubuce-rubuce na adabi.
Wane ne ya fara taimaka maka wajen ba ka shawarwari ko gyare-gyare don inganta rubutunka?
Wacce ta fara taimaka min wajen inganta rubutuna ita ce wata marubuciya ce ana ce mata, Fatima Y. Zakariyya. A gaskiya ta taka muhimmiyar rawa ƙwarai a farkon tafiyata ta fannin adabi, inda take ba ni shawarwari masu amfani, gyare-gyare a kan tsarin labari da amfani da kalmomi, gami da ƙwarin gwiwar da ya gina gogewata har na samu damar faɗaɗa basirata a fagen rubutu.
Tsakanin karatu da rubutu wanne ka fi yi?
Gaskiya karatu na fi yi. Ba mai yiwuwa ba ne mutum ya zama marubuci mai zurfin tunani ba tare da ya kasance mai karatu ba. Duk littafin da na karanta yana faɗaɗa tunanina, yana ƙara mini ilimin amfani da kalmomi, kuma yana ba ni sabbin damarmaki na fahimtar ɗan’adam da al’umma. Saboda haka, karatu shi ne kashi saba’in na tafiyata, yayin da rubutu ke zamowa sakamakon abubuwan da na karanta.
A cikin littattafan da ka karanta wanne ne ya fi yin tasiri akan ka, har ka ji kana so kaima ka zama marubuci?
Littafin da ya fi kowanne yin tasiri mai zurfi a zuciyata har ya rura wutar son zama marubuci a tare da ni shi ne, ‘Idan An Ciza… wanda wata shahararriyar marubuciya Janafty ta rubuta.
Kawo yanzu littattafai nawa ka rubuta? Kawo sunayensu da bayani kan uku daga ciki.
A halin yanzu dai cikin ikon Allah na rubuta littattafai dogaye guda huɗu, da kuma gajerun labarai guda biyar. Littattafan su ne, ‘Tudu A Kwari’, ‘Hasashen Soyayya’, ‘Sartse’, da kuma ‘Sakata’. Su kuma gajerun labaran su ne, ‘Da Na Sani’, ‘Haske Daga Duhu’, ‘Gobe Da Nisa’, ‘ƙarar ƙaho A ƙauye’, sai kuma ‘Wata Bautar’.
Shi labarin Da Na Sani, labari ne a kan wani matashi da gaskiya ta ba shi damar ɗaukaka, amma zuga da ruɗin abokain banza suka kai shi ga aikata nadama da da na sani a rayuwa.
Shi kuwa littafin Haske Daga Duhu labari ne a kan wata matashiya da ta fito daga ƙauye zuwa birni domin neman ilimi da haskaka rayuwarta da ta al’ummarta.
Sartse kuma labari ne mai ƙarfi da ke ba da labarin rikitattun al’amuran soyayya, tsamin da ke iya shiga tsakanin masoya, da yadda ƙalubalen rayuwa ke gwada jajircewar ɗan’adam.
Wanne salon rubutu ka fi mayar da hankali akai, tsakanin labaran soyayya, jarumta, tarihi, da almara?
Na fi mayar da hankali sosai a kan labaran soyayya da zamantakewa. Dalili kuwa shi ne, soyayya da zamantakewar al’umma su ne ginshiƙin da kowane ɗan’adam ke rayuwa a kansa. Ta hanyar soyayya, mutum yana iya isar da saƙonni masu gina tarbiyya, warware matsalolin ma’aurata, da ba da shawarwari kan yadda za a fuskanci ƙalubalen rayuwa cikin sauƙi.
Yaya ka ke samun jigon da ka ke yin rubutu a kai?
Ina samun jigon rubutuna ne daga abubuwan da ke faruwa a cikin al’umma na yau da kullum, gogewar da nake samu a kasuwanci da hulɗa da mutane, gami da zurfafa tunani wajen karanta littattafai da kallo. Wani lokaci kuma matsalar da na ga wani ke fuskanta takan zama wutar da ke hura mini tunanin tsara labari domin samar da mafita ga sauran al’umma.
Wanne goyon baya ka ke samu a gida da wajen abokai game da rubuce-rubuce da karatu ke yi? Ka taɓa fuskantar wani ƙalubale daga gare su?
Ina samun goyon baya sosai a gida, musamman daga mahaifina wanda ke ƙara mini ƙwarin gwiwa da shawarwari kan amfani da kalmomi masu inganci. Abokai ma suna ba ni goyon baya sosai. A farkon tafiya ana iya samun ƙalubale na rashin fahimta daga wasu da ke ganin kamar rubutu yana ɓata lokaci, amma da zarar sun fara ganin sakamako da amfanin sa ga al’umma, sai ƙalubalen ya koma goyon baya.
Wanne rubutu ne ka taɓa yi wanda ya zama maka alaƙaƙai, ka kasa cigaba da rubutun, kuma ka kasa jinginewa? Yaya ka warware matsalar?
Littafina mai suna Sartse ya ɗan zama mini alaƙaƙai a tsakiya, saboda zurfin sarƙaƙiya da saƙon da yake ɗauke da shi na buƙatar takatsantsan. Na kai matakin da na kasa cigaba saboda nauyin labarin, amma kuma ban iya jingine shi ba saboda irin ƙaunar da nake yi masa. Na warware matsalar ne ta hanyar ɗaukar hutu daga rubutun, na mayar da hankali wajen karanta sauran littattafai da neman shawarar wasu manyan marubuta, har dai tunanina ya washe na dawo na ƙarasa shi cikin nasara. Alhamdulillah.
Mene ne alaƙarka da masu bibiyar rubutunka? Yaya ka ke fahimtar masu karatu na jin daɗin labarinka?
Alaƙata da masu karanta rubutuna alaƙa ce ta amintaka, girmama juna, da kuma karɓar gyara. Ina fahimtar suna jin daɗin labarina ta hanyar tsokaci (comments) da suke yi a dandalolin karatu, saƙonnin da suke turo mini na ƙashin kai, da kuma yadda suke nuna ƙishirwar jiran fitowar shafi na gaba.
A cikin masu karanta littattafanka wani ya taɓa baka wata shawara da ta taimake ka a rubutun ka, ko wani alheri da ba za ka manta ba?
ƙwarai kuwa! Wata ma’abuciyar karatu ta taɓa ba ni shawara a kan yadda zan faɗaɗa salon gina muhalli da halayyar mutanen cikin labarina, maimakon mayar da hankali a kan magana kawai. Wannan shawarar ta buɗe mini idanu ƙwarai wajen inganta salon rubutuna. Haka zalika, addu’o’in alheri da ƙwarin gwiwa daga masu karatu abubuwa ne da ba zan taɓa mantawa da su ba.
Yaya ka ke mu’amala da kafafen sada zumunta wajen yaɗa rubuce-rubucenka? Waɗanne shafuka ko zauruka ka ke amfani da su?
Ina amfani da zaurukan sada zumunta da na karatun zamani sosai wajen baza rubuce-rubucena. Ina amfani da manhajoji irin su, ArewaPen, da Hikaya Bakandamiya, gami da shafukana na Facebook da WhatsApp wajen tallata littattafai, samun ra’ayoyin masu karatu, da isar da saƙonni.
Shin kana amfani da fasahar AI a rubutunka? Yaya tasirin fasahar ga marubuta adabin Hausa?
Ina amfani da fasahar AI sosai kuwa, musamman wajen samar da hotunan bangon littattafaina (coɓer designs), haɗa sauti da bidiyon tallata littafi, da kuma bincike a kan rubutun da nake yi. Amma wajen gina labari da saƙa rubutu, gini da hawa da saukan labari, basirar AI ba za ta taɓa yin abin da basirar ɗan’adam za ta yi ba. Tasirin AI ga marubuta adabin Hausa yana da kyau ƙwarai idan aka yi amfani da shi wajen sauƙaƙe tallata littattafai da faɗaɗa bincike, amma bai kamata ya maye gurbin basira da ƙirƙira ta ainihi ba.
Wacce shawara ka ke da ita ga marubutan Hausa kan yadda za su ci moriyar fasahar AI?
Shawarar da zan ba marubuta Hausa ita ce su ɗauki fasahar AI a matsayin mai taimaka musu wajen aiki, ba wanda zai karɓe musu basirarsu ba. Suna iya amfani da ita wajen yi wa littafi kyakkyawan bango, ƙirƙirar sautuka da bidiyoyi na tallata littafi, da gudanar da bincike akan jigon da suke so su yi rubutu a kai.
Kana sha’awar rubuta labarin fim, ko ka taɓa rubuta wasu?
Gaskiya a halin yanzu ban da sha’awar rubuta labarin fim. Hankalina da tunanina gaba ɗaya suna karkata ne a kan rubutun zube da gajerun labarai, domin ta nan ne na fi jin sauƙin bayyana saƙonni da zurfin adabina ta hanyar da mai karatu zai ƙulla alaƙa ta kai tsaye da labarin.
Me ya sa akasari marubuta maza suke ƙaurace wa rubutun zube zuwa na fim?
Gaskiya ban san takamaimen dalilansu ba, amma a nawa hangen, ina ganin babban dalilin da ke sa marubuta maza suke karkata zuwa rubutun fim shi ne batun riba da kasuwanci. Fanni ne da ke saurin dawo da jarin da aka zuba da samun alawus mai tsoka daga masu shirya finafinai, saɓanin rubutun zube wanda ke buƙatar tsawon lokaci, haƙuri, da juriya kafin a samu sakamakon abin da aka shuka.
Ka taɓa shiga wata babbar gasar rubutun adabi da ka yi nasara a cikinta? Kawo sunanta, taken labarin da shekarar?
E. Na fara shiga babbar gasar rubutu ta Gusau Institute a shekarar 2026. Cikin ikon Allah, labarina ya samu nasarar tsallake zagaye na farko, kuma a halin yanzu muna jiran sakamakon ƙarshe na gasar.
Ina aka kwana a ƙoƙarin kafa ƙungiyar maza marubuta? Mene ne matsayinka a tafiyar kuma wanne tanadi ku ke da shi na haɗa kan marubuta maza?
A halin yanzu an samu nasarar kafa ƙungiyar marubuta maza mai suna, Majalisar Adabin Hausa. Ni ne ke taka rawa a fannin jagoranci da tsara al’amuran tafiyar. Sannan muna da tunanin samar da dandali guda ɗaya da zai haɗe kan marubuta maza, ƙarfafa musu gwiwa, shirya bita, da gudanar da bincike na haɗin gwiwa, domin gina juna da ɗaga darajar adabin Hausa.
Gaya mana babban burinka nan gaba a rayuwa?
Babban burina a rayuwa shi ne in zama marubuci mai tasiri wanda rubutunsa zai gina al’umma, in mallaki babban kamfanin kasuwanci wanda zai samar da ayyukan yi ga matasa, sannan in zama ɗan kasuwa wanda zai tallafa wa cigaban al’ummarsa.
Idan Allah Ya ba ka dama wacce ƙasa ka ke sha’awar kai ziyara?
Ina sha’awar ziyartar ƙasar Saudi Arabia domin gudanar da aikin Hajji da Umrah da samun albarka. Sannan ina sha’awar ziyartar ƙasashe irin su Chana ko Dubai, domin ganin cigaban kasuwanci, da ƙarin ilimi.
Me ka fi son yi a lokacin da ka ke cikin nishaɗi?
A duk lokacin da nake cikin nishaɗi babu abin da nake son yi sama da rubutu, a wannan lokacin tunani na ya fi ba ni abu mai kyau.
Su waye manyan abokanka ko ƙawaye da ku ke zumunci sosai cikin marubuta?
Ina da kyakkyawar alaƙa da zumunci mai ƙarfi da ‘yan’uwa marubuta da dama. Daga cikin na kusa da ni sosai akwai marubuta irin su Janafty, Sadeeƙ ɗanguguwa, Ummulkhairi Sani Panisau, Maryam Aminu, Fatima Musa da Fatima Isa Manu. Waɗannan su ne marubutan da na kan yi shawara ko tattaunawa da su sama da kowa. Haka zalika, ina zumunci da haɗin gwiwa tare da mambobin ƙungiyar Future Writers Association da kuma ‘yan’uwana na ƙungiyar marubuta maza, Abba Ubale Kibiya, Jibril Yusuf Kaila, da Dr Isham.
Me ya fi burge ka da rayuwa cikin marubuta, kuma me ya fi baka haushi?
Abin da ya fi burge ni da ƙayatar da ni a rayuwar marubuta shi ne tsantsar zumunci, girmama juna, da kyakkyawar alaƙa. Abin da kuma ya fi ba ni haushi shi ne ƙananan maganganu, da kuma faɗa marar tushe. Marubuta ‘yan’uwan juna ne, amma kowa da ‘yan ɗakinsu.
Ka taɓa nadamar zama marubuci?
A’a, har abada ban taɓa yin nadamar zama marubuci ba, kuma ba na fatan yin nadamar kasancewa ta marubuci. Marubuta da rubutu sun zama tamkar jinin da ke yawo a jikina. Kasancewa ta marubuci wata babbar dama ce da ke ba ni ikon tunani mai zurfi, isar da saƙonni masu amfani.
Wacce karin magana ce take tasiri a rayuwarka?
Karin maganganun da suka fi yin tasiri a rayuwata su ne, ‘Idan kaya ya gaji to, gammo ma ya gaji’, wanda ke tunatar da ni haƙuri da fahimtar cewa kowa yana da irin nasa ƙalubalen a rayuwa. Sai kuma karin maganar da ake ce wa, ‘Sannu sannu ba ta hana zuwa, sai dai a daɗe ba a je ba’, wadda ke koya mini juriya, jajircewa, da kuma amincewa cewa matakai na sannu-sannu sune ke kai ɗan’adam ga nasara mai ɗorewa.
Masha Allah. Ina godiya ƙwarai da gaske.
Ni ne da godiya. Na gode da damar da aka ba ni.
