Shugabannin masu ruwa da tsaki a jam’iyyar APC na ƙananan hukumomin Jihar Katsina sun amince da jagorancin Gwamna Dikko Umaru Raɗɗa tare da yaba wa salon jagorancin sa da nasarorin da gwamnatin sa ta samu cikin shekaru uku da suka gabata.
Shugaban ƙungiyar, Alhaji Salisu Mamman Continental, ya ce gwamnatin Raɗɗa ta samu ci gaba a fannonin ilimi, lafiya, noma, ababen more rayuwa da bunƙasa tattalin arziki, tare da dawo da amincewar jama’a ta hanyar gaskiya, riƙon amana da haɗa kan al’umma.
Ya kuma gabatar wa Gwamnan rahoton rangadin da suka gudanar a mazaɓu 15 na tarayya, inda suka gana da masu ruwa da tsaki tare da sauraron yanayin da jam’iyyar take a matakin ƙasa. Ya ce dukkan ƙananan hukumomi 34 na jihar suna da tsarin wayar da kan jama’a da samar da al’umma (mobilization) tun daga ƙananan hukumomi har zuwa matakin rumfunan zaɓe.
A nasa jawabin, Gwamna Raɗɗa ya gode wa shugabannin bisa jajircewa da biyayya ga jam’iyya, tare da buƙatar su ƙara ƙarfafa haɗin kai wajen tunkarar zaɓen 2027.
Gwamnan ya kuma buƙaci su yi cikakken tuntuɓar mutane (mobilization) domin samun nasarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu da dukkan ƴan takarar APC a Katsina, yana mai cewa haɗin kai da aiki tare su ne ginshiƙan samun nasara.
