Kwalliya ko barazana: Lokacin da neman hasken fata ke zama haɗari

Spread the love

Daga AISHA ASAS

Akwai lokacin da mace take kallon fuskarta a madubi, sai ta ga wani ɗan tabo, baƙin gwiwa, ƙuraje ko kuma canjin launin fata. Sai ta fara neman abin da zai sa fatar ta yi laushi, ta daidaita launinta ko kuma ta ƙara haske. 

Wani lokaci ma ba wata matsala ce take damunta ba; kawai ta ga wata ƙawarta ta canza launin fata, ko ta ga wata fitacciya a kafafen sada zumunta, sai ita ma ta ji tana son irin wannan canjin.

A nan ne wata tambaya ke da matuƙar muhimmanci, wato ta yaushe neman kyau yake daina zama kulawa da kai, ya koma abin da zai iya cutar da kai?

Domin abin da mace take shafawa a jikinta yau saboda tana son ta yi kyau, ba lallai ne ta ga illarsa nan take ba. Wasu sinadarai na iya yin aiki a hankali, har sai bayan watanni ko shekaru ne matsalar ta fara bayyana.

Mai karatu barkanmu da sake kasancewa a shafin Kwalliya na jaridar Blueprint Manhaja. Sannunku da jimirin bibiyar mu. 

A wannan makon za mu tattauna ne game da kayan haskaka fata da ake amfani da su domin sauya launin fata, da kuma yadda neman fata mai haske zai iya zama barazana ga lafiyar mutum.

Me ya sa ake son sauya launin fata?

Launin fatar ɗan adam yana da alaƙa da wani sinadari da ake kira melanin. Shi ne ke ba fata launinta kuma yana taimaka wa wajen kare fata daga wasu illolin hasken rana.

WHO ta bayyana cewa kayan haskaka fata suna aiki ne ta hanyar rage yawan whi wannan sinadarin na melanin da fata ke samarwa. Amma hukumar ta kuma yi gargaɗin cewa wasu daga cikin waɗannan kayayyaki na iya ɗauke da sinadarai masu haɗari, musamman mercury.

Saboda haka, ba duk wani abu da aka rubuta masa ‘brightening’, ‘lightening’, ‘toning’, ‘whitening’ ko makamancin haka ne mutum zai iya ɗauka cewa ba shi da matsala ba.

A shekarar 2026 ma, WHO ta sake fitar da wani sabon tsarin bincike kan amfani da kayan haskaka fata, inda ta bayyana cewa amfani da waɗannan kayayyaki yana da alaƙa da abubuwa da dama, ciki har da ra’ayoyin al’umma game da kyau, tallace-tallace da matsin lambar zamantakewa.

Wato, a wasu lokuta abin da yake sa mace ta nemi sauya launin fatarta ba wai matsalar fata kawai ba ce; har ma da yadda ake kallon kyau a cikin al’umma.

Shin duk kayan haskaka fata suna da haɗari?

Amsar kuwa ita ce a’a. Kuma yana da matuƙar muhimmanci mu san bambancin. 

Ba daidai ba ne a ce duk wani kayan kula da fata da aka yi wa laƙabi da ‘brightening’ zai cutar da mutum. Matsalar ita ce wasu kayayyaki suna iya ƙunsar sinadarai masu ƙarfi ko haɗari, wasu kuma ana iya amfani da su ba tare da sanin abin da ke cikinsu ba.

Masu bincike sun gano cewa wasu kayan haskaka fata na iya ƙunsar hydroƙuinone, corticosteroids ko mercury. Wani binciken da aka yi kan kayayyakin haskaka fata da aka samu a kasuwannin wasu ƙasashen Afirka ta Yamma ya gwada sabulai 93 da man shafawa 98, inda ya gano cewa kaso mai yawa na wasu kayayyakin ya wuce ƙa’idojin da aka tsara na ɗaya ko fiye daga cikin sinadaran da aka bincika.

Wannan ya nuna cewa matsalar ba ta tsaya ga abin da aka rubuta a jikin kwalba kawai ba. Wani lokaci sai an gwada samfurin a ɗakin bincike ne za a tabbatar da ainihin abin da yake cikinsa.

By ukarofi

Leave a Reply