
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid ta fara kakar wasannin Kofin Zakarun Nahiyar Turai UEFA Champions League ta 2026/27 na ƙafar dama bayan samun nasara akan Inter Milan ta ƙasar Italiya da ci 2 da 1 a ranar Talata.
Ita ma Manchester City da ta je ƙasar Portugal, ta doke FC Porto da ci 1 mai ban haushi yayin da aka yi ruwan ƙwallaye, farfaɗowa da kuma zura ƙwallo cikin salo masu ban ƙaye a sassan nahiyar.
Haka ƙungiyoyin Borussia Dortmund, Real Betis, Aston Villa da AEK Athens sun yi nasarori a wasanninsu, inda Vill ta yi nasara da ci 3-2 a karawarta da Club Brugge, sai Betis da ta farfaɗo tare da samun nasara kan Lille a ɗaya daga cikin wasannin da suka ƙayatar.
Real Madrid ta yi nasara ne a wasanta da Inter ta hannun Kylian Mbappe a minti na 14, sannan bayan minti tara ne Fede Valverde na ƙasar Uruguay ya zura ta biyu. Bayan koma wa hutun rabin lokaci ne sai Inter ta samu damar farke ɗaya ta hannun Carlos Agusto da gudunmawar Lautaro Martinez.
A wani wasan kuwa, Borussia Dortmund ta Jamus ta doke Villarreal da ci 3 da 1 bayan farfaɗowa daga ƙwallon da ƙungiyar Sifaniyar ta zura mata a zangon farko na wasan. A ranar farkon dai an zura jimillar ƙwallo 18 a raga inda Real Madrid, Manchester City, Dortmund, Betis, Aston Villa da AEK suka fara kakar da ƙafar dama.
Za kuma a cigaba da wasannin rukunin a ranar Laraba, yayin da za kara tsakanin Paris Saint-Germain da Slovan Bratislava, Barcelona da Feyenoord, Liverpool da Atletico Madrid, Sporting CP da Galatasaray, sai kuma Napoli da Arsenal mai riƙe da Premier League.
