Jami’ar NOUN ta naɗa Ramatu Ibrahim a matsayin jami’ar kuɗi ta riƙo bayan kisan Marafa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Jami’ar National Open University of Nigeria (NOUN) ta naɗa Ramatu Ibrahim a matsayin jami’ar kuɗi ta riƙo bayan rasuwar ainihin mai riƙe da muƙamin, wato Nasir Marafa.

Rahotanni sun bayyana cewa, an gudanar da naɗin, wanda ya fara aiki a nan take ne jim-kaɗan bayan Marafa ya rasu sakamakon harbe shi da aka yi a lokacin da yake kan hanyar komawa daga Gusau, babban birnin jihar Zamfara.

Mataimakin Shugaban jami’ar (VC), Farfesa Uduma Oji Uduma tare da Shugaban majalisar jagororin jami’o’i, Malam Isa Yuguda ne suka amince da naɗin, yayin da Rajistaran jami’ar, Oladipi Ajayi ya sanar da haka a ranar Talata cikin wata takarda. A cewar Ajayi, an yi wannan naɗi ne da nufin tabbatar da cigaba da ɗorewar jagoranci mai inganci a harkokin kuɗin jami’ar.

Misis Ramatu gabanin yanzu, ta riƙe muƙamin mataimakiyar jami’in kuɗi da asusu kuma ɗaya ce daga cikin manyan jami’an gudanarwar kuɗaɗen jami’ar.

A ranar Lahadi ne wasu ‘yan bindiga suka harbe Marafa yayin da yake koma wa jami’ar daga Gusau, a cewar wata sanarwa da Oladipo Ajayi ya fitar. Saidabai bayyana haƙiƙanin inda da yadda al’amarin ya auku ba.

By Babaji

Leave a Reply