
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Mataimakin daraktan harkokin yaɗa labarai a Fadar Shugaban Ƙasa, Peter Onwubuariri mai shekaru 48 ya rasu a Kano bayan tsawon lokaci yana jinya.
Rahotanni sun bayyana cewa, Onwubuariri, wanda daɗaɗɗen ɗan jarida kuma mamba a Kamfanin Dillancin Labarai NAN, ya rasu ne a ranar Litinin bayan zaman karɓar magani na kusan wata guda a asibitin Kano Cancer Hospital a ƙarƙashin ikon gwamnatin jihar. Matar marigayin, Catherine Ezinn Onwubuariri ce ta tabbatar labarin mutuwarsa.
A ranar Talata ne aka sako gawarsa daga Asibitin Koyarwa na Aminu Kano domin yi mata jana’iza a Owerri, Jihar Imo. An damƙa ta ne ga Mataimakin Daraktan Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na Fadar Shugaban Ƙasa, Oche Egwa a madadin Mai ba Shugaban Ƙasa Shawara akan Harkar Yaɗa Labarai da Dabaru, Bayo Onanuga ta hannun Kakakin Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, Sanusi Bature Dawakin Tofa a hukumance.
Wannan al’amari ya sanya Shugaba Tinubu bayyana kaɗuwarsa, yana mai bayyana mutuwar ɗan jaridar kuma jami’in gwamnati a matsayin rashi mai raɗaɗi ga Fadar Shugaban Ƙasa da NAN da fagen jarida da ma ƙasa baki ɗaya.
A sanarwar da Onanuga ya fitar a Talata, Shugaban ya ce Onwubuariri, wanda tsohon wakilin Amurka ta Arewa ne na NAN, an tura shi aiki ne a fadar shugaban ƙasa tun a shekarar 2014, kuma ya yi hidima ƙarƙashin gwamnatocin Goodluck Ebele Jonathan, Muhammadu Buhari da Bola Tinubu.
Ya bayyana cewa, za a cigaba da tuna marigayin a matsayin jajirtacce kan aikinsa, ƙwararre da kuma gudunmawar da ya bayar ga harkar jarida da hidimar ƙasa.
A ƙarshe, Tinubu ya miƙa gaisuwar ta’aziyyarsa ga matarsa Catherine, ‘ya’yansa uku, danginsa, abokan aiki da abokan arziƙi, yana mai addu’ar Ubangiji ya bai wa iyalan nasa haƙurin juriyan rashin sa, ya kuma jiƙan marigayin.
