Gwamnatin Kebbi ta rushe jagorancin hukumar zaɓe ta jihar

Spread the love

Gwamnatin jihar Kebbi ƙarƙashin jagorancin Malam Nasir Idris ta sanar da rushe jagorancin hukumar zaɓe mai zaman kan ta ta jihar Kebbi (KESIEC).

Wannan yana ƙunshe ne a wata takarda mai ɗauke da da hannun sakataren gwamnatin jihar Alhaji Yakubu Bala Tafida ranar Talatar nan.
Takardar ta bayyana cewa rushe jagorancin hukumar ya biyo bayan cikar wa’adin ta ne da ya yi daidai da ranar 18 ga watan Satumba na wannan shekarar ta 2026.

Takardar ta bayyana cewa sai dai akwai mambobi biyu ta wa’adin aikin su bai cika ba su za su cigaba da aiki tare da sababbin da za a naɗa nan gaba kaɗan.

Takardar ta bayyana godiyar gwamna Malam Nasir Idris ga waɗannan mutanen bisa ga irin ƙoƙarin da suka yi a lokacin zaman su a wannan ofis na kare martabar ta tare da yiyuwar duba fasalin yadda za a sake sabon zubi.

By ukarofi