
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A ranar Talata Alhaji Shehu Kabiru Bayero, wanda shi ne Hakimin Ɗorayi kuma Barde Ƙerarriya a Masarautar Kano, ya rasu a Misra.
Masarautar Kano ce ta sanar mutuwarsa a wata takarda da ta aike wa manema labarai a yammacin Talata, inda ta bayyana jimaminta bisa rasuwar basaraken kuma tsohon kwamishinan ‘yan sanda. A sanarwar, an yi addu’ar Allah ya jiƙan marigayin ya kuma bai wa iyalansa da Gidan Sarautar Kano haƙurin juriyan rashin sa.
Saidai masarautar ba ta bayyana lokacin da za a kawo gawar marigayin gida Nijeriya ba domin ya mata jana’iza.
A shekarar 2025 Sarkin da aka dawo shi kan karagar mulki, Muhammadu Sanusi na II, ya sauya wa Kabiru Bayero guri daga Gwarzo, zuwa sabuwar gundumar Ɗorayi da aka samar.
Da fari marigayi Sarki Ado Bayero ne ya naɗa shi a matsayin Barde Ƙerarriya a shekarar 2006, kuma aka mayar da shi Hakimin Gunduma a Ƙaramar Hukumar Takai kafin daga bisani aka sake tura shi zuwa Gwarzo.
A matsayinsa na tsohon kwamishina, marigayi Shehu Kabiru ya shiga aikin ɗan sanda a shekarar 1970 a matsayin kurtu, kana ya cigaba samun muƙami har zuwa kwamishin, inda ya yi aiki a jihohin Gombe da Osun kana ya yi murabus bayan shafe shekaru 35 yana aiki. Sannan, an haife shi ne a shekarar 1949 har ya kai matakin kwamishina kana ya yi ritaya a 2004.
