Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Allah yayi wa tsohon Sanata Bello Mandiya rasuwa a daren litini a gidansa da ke Abuja.
Babu wani bayani game da rasuwar sa.
Kafin rasuwar Sanata Bello Mandiya ya wakilci shiyar Funtua a majalisar dattijai ƙarkashin jam’iyar APC a Jihar Katsina.
Sanatan ya taɓa rike muƙamin shugaban ma’aikatan gidan gwamnnatin Katsina.
Gwamna Dikko Raɗɗa ya ce ya kaɗu ƙwarai da ya sami labarin rasuwar Bello Mandiya.
Ya bayana rasuwar sanatan a matsayin babban asara ba ma ga alummar jihar ba har ma ga ƙasa baki ɗaya.
Yayi fatan Allah kai rahama ga kabarinsa.
