Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Ɗan takarar gwamna a Jihar Zamfara a jam’iyyar African Democratic Congress, ADC, Hon. Bilyaminu Yusuf Shinkafi, ya ce tsaron rayuka da dukiyoyi alumma zai zama babban abin da gwamnatinsa za ta sa a gaba idan aka zaɓe shi a 2027.
Shinkafi ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi a wani taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar da aka gudanar a Kaduna.
A cewarsa, rashin tsaro a Zamfara yana bukatar hanyar hadin gwiwa kuma ba za a iya barin gwamnati ita kaɗai ba.
“Tsaro nauyi ne na haɗin gwiwa. Zan yi amfani da duk wata hanya da ake da ita ta hanyar jawo hankalin dukkan masu ruwa da tsaki don daƙile matsalar rashin tsaro idan aka zaɓe ni a matsayin gwamnan Jihar Zamfara a ƙarƙashin ADC,” in ji shi.
Shinkafi ya ƙara da cewa gwamnatinsa za ta ba da fifiko ga hadin gwiwar al’umma, tattara bayanan sirri, da haɗin gwiwa da sarakunan gargajiya, hukumomin tsaro, da ƙungiyoyin fararen hula don magance rikicin da ke ci gaba da addabar jihar.
Da yake magana kan babban zaɓen 2027, Shinkafi ya bayyana ƙwarin gwiwar cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC, tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar, zai samu goyon baya mai ƙarfi a Arewa maso Yamma.
“Muna da tabbacin idan Allah ya yarda Atiku zai samu kashi 40 cikin 100 na ƙuri’un da aka kaɗa a Arewa maso Yamma, a ƙarƙashin ADC a babban zaɓe mai zuwa,” in ji shi.
Shinkafi ya gode wa mambobin jam’iyyar ADC da magoya bayanta a Zamfara saboda goyon bayansu mara misaltuwa, wanda ya haifar da fitowarsa a matsayin ɗan takarar gwamna na jam’iyyar.
Ya kuma yaba wa hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa, INEC, saboda amincewa da shi a matsayin wanda zai ɗauki tutar jam’iyyar ADC a Zamfara.
Ya ce manufar taron na Kaduna ita ce a haɓaka haɗin kai da kuma sake tsara jam’iyyar don samun nasara a 2027.
“Ina kira ga dukkan membobin jam’iyyarmu da suka fusata da su haɗu wuri ɗaya. Manufarmu ɗaya ce, don tabbatar da nasarar jam’iyyar ADC a Zamfara da kuma a matakin ƙasa,” in ji shi.
Shugabannin jam’iyyar a taron sun yi alƙawarin neman goyon baya daga jama’a a faɗin ƙananan hukumomi 14 na Zamfara kafin zaɓen.
