Yaƙin neman zaɓe: Ya kamata malamai su riƙe girman su 

Spread the love

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

A yayin da ake cigaba da kusantar lokacin Babban Zaɓen 2027, jama’a na cigaba da bayyana ra’ayoyin su game da batutuwan da suka shafi ’yan takara da jam’iyyun siyasa ko wasu manufofi da ke kare muradun waɗanda suke goyon baya. Kuma ga mai nazarin abubuwan da suke faruwa zai fahimci cewa tuni an riga da an ja layi, akasarin ’yan Nijeriya sun yi wa kan su matsaya game da ra’ayi ko fahimtar da ta fi kwanta musu a rai.

An fahimci muhimman abubuwan da ake sa ran za su yi tasiri a yaƙin neman zaɓen da ke tafe, duk da yake Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta INEC ta fitar da sharuɗɗa da ƙa’idojin yadda za a tafiyar da yaƙin neman goyon bayan masu zaɓe, abubuwan da ta ƙayyade da wanda ta hana. Amma tuni jama’a na ci gaba da yin gaban kansu, ko ƙoƙarin bin yanke hanya da dabarun sauya tsari, duk dai domin dai ya biya buƙatunsu.

Wani ɓangare mai muhimmanci da zai ɗauki hankalin jama’a a yayin yaƙin neman zaɓen da aka shiga bayan ƙoƙarin raba kan jama’a kan taɓarɓarewar tsaro, da amfani da talaucin da ake fama da shi, wajen rabon abinci ga mabuƙata ko wani tallafi mai muhimmanci, sai batun rawar da addinai za su taka wajen nuna goyon baya ga wasu ýan takara da suke kallon nasu ne. Ko dai masu taimaka musu wajen ba da tallafin kuɗaɗe ko kuma domin addininsu ɗaya. 

Tuni ma dai mun ga yadda aka fara samun shugabannin ƙungiyoyin addinai suna ta rige-rigen zawarcin manyan ’yan takarar da ake ganin za su yi tasiri a zaɓen da ke tafe, ko dai da sunan zuwa ba su shawarwari, gayyatar su taruka da sunan ba da shawarwari kan yadda za a inganta tsaro ko zaman lafiya, ko kuma da sunan karrama su kan nasarorin da suka samu a wasu ɓangarori na cigaban ƙasa. Waɗannan duk ana yi ne da nufin tallan ɗan siyasa a fakaice, ba tare da an fito kai tsaye an nuna me ake so a yi ba.

Irin waɗannan tarukan sun faru akan idanun gwamnati da jama’ar ƙasa, amma an kawar da kai an yi kamar babu abin da ke faruwa. Wasu abubuwan ma da ake yi, irin abin nan ne da ake cewa, makoyi ya fi mahori. Domin sun faru a baya, kuma an ga illar hakan, amma an kasa ɗaukar darasi.

A kwanakin baya ne aka gudanar da wani taron malamai game da matsalolin tsaro da ke addabar jihohin yankin Arewa, wannan dai taron da aka gudanar a Jigawa. A ƙarshen taron mun ji yadda kafafen watsa labarai suka riƙa yaɗa cewa, malamai a Arewa sun goyi bayan tazarcen shugaban ƙasa Bola Tinubu. Kodayake daga bayan an samu wasu malamai da suka fito suka musanta cewa ba haka aka yi da su ba. Wannan na bayyana mana yadda waɗannan ’yan siyasa ke ƙoƙarin bin kowacce irin hanya, don dai haƙar su ta cimma ruwa.

Mun ga wasu tarukan irin waɗannan a Jos da Abuja, kuma duk domin sharar fage ne ga babbar hidimar da ke tafe. A ganina, malamai ko fastoci, iyayen al’umma ne, waɗanda shawarwarinsu da addu’o’in su suke da matuƙar muhimmanci ga cigaban ƙasa da zaman lafiyarta. Ba haƙƙinsu ba ne su nuna goyon baya ga wani ɗan takara ko wata jam’iyyar siyasa. Ba ina nufin malami ba shi da ’yancin faɗin ra’ayinsa na siyasa ko shiga a dama da shi ba, ina cikin masu goyon bayan malamai da fastoci su shiga siyasa ko sha’anin mulki don kawo tsafta a shugabanci, adalci, da kiyaye haƙƙoƙin ’yan ƙasa a matsayin su na masu kira ga kyautata halaye da tsoron Allah. Matuƙar malami ko mai wa’azi zai shiga siyasa ya tsare kimarsa da mutuncin abin da yake wakilta, ban ga laifi a nan ba.

Amma a yi gungu da sunan ƙungiyar addini a shirya taro da sunan bayyana goyon baya ga wata jam’iyyar ko ɗan takara, da sunan al’ummar Musulmi ko wani yanki, ina ganin akwai kuskure a ciki.

Na ga wani bidiyo da yake yawo a zaurukan sada zumunta, inda wani malamin addinin Musulunci yake huɗuba a wani taro, har yana cewa musu komai zaluncin shugaba, ko da ana yunwa da kashe-kashe a mulkinsa, addini bai yarda a yi masa tawaye, ko a bijire masa ko a zarge shi ba, domin Allah ne Ya ba shi mulkin. Kodayake ban saurari har zuwa ƙarshen wa’azi ba, amma ban ji inda malamin ya karanta wata aya ko hadisi da ke tabbatar da ingancin abin da ya bayyana ba.

Na sani abin da ya faɗa ra’ayin sa ne kuma ya cancanci faɗin hakan, amma in so samu ne kar ya faɗa a masallaci, domin nan farfajiya ce ta addini inda ake da mabiya masu bambancin ra’ayin siyasa da fahimtar rayuwa. Yana da kyau malamai da fastoci da sauran shugabannin al’umma su riƙa yi wa bakin su linzami, kada garin neman burge wani, mutum ya ja wa kansa zagi ko cin mutunci daga waɗanda suke ra’ayi daban da nasa.

Wasu rahotanni sun bayyana cewa wasu fusatattun matasa su ci mutuncin wani malami da yake wa’azin goyon bayan gwamnati a cikin masallaci. Wannan abu ne na rashin ɗa’a da bai kamata ba, amma kuma shi malamin shi ya ba da damar yin abin da waɗannan matasa ke ganin daidai ne a fahimtar su, musamman ganin ƙalubalen tsaro da jihar su ke fuskanta. 

Ya kamata malamai sun fi kowa sanin cewa a irin tsarin da ƙasar nan ke ciki, kuskure ne a riƙa ganin masu addini da ’yan siyasa suna cakuɗewa wuri ɗaya a bainar jama’a. Sannan haka a cikin karatu ko wa’azi a guji shigar da batun da zai nunawa jama’a ƙarara cewa ga inda malam wane ya fi karkata. Siyasa zaɓin mutum ne, kuma shi kaɗai yake da wannan ’yancin bisa raɗin kansa. Ganin damarsa ne ya amince ko akasin haka. Kuma malamai a matsayin su na jagororin al’umma ba za su wakilci wannan ra’ayin a madadin mabiyansu ba.

Amfani da addini wajen yaƙin neman zaɓe kuskure ne mai girma a halin da ƙasar nan ke ciki. A ƙyale kowa ya zaɓi wanda ya ga ya fi cancanta ya wakilce shi a kowanne mataki na mulki. Allah kuma shi yake bayar da mulki ga wanda ya so.

Fatan mu shi ne, Allah Ya ba mu shugabanni masu adalci da tausayin talakawansu.

By ukarofi

Leave a Reply