
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A ranar Litinin mijin Shugaba Samia Suluhu Hassan ta ƙasar Tanzaniya, Hafidh Ameir ya rasu yayin da yake karɓar magani a wani asibiti da ke Birnin Zanzibar.
BBC ta ruwaito cewa, Mataimakin Shugaban ƙasar, Deogratius Ndejembi ne ya sanar da rasuwa Ameir, inda ya ce ya kasance yana fama da wata cuta da ta shafi zuciya.
Ndejembi ya ce, Ameir ya rasu ne da misalin ƙarfe 8:00 na safiyar Litinin a Asibitin Emilio Mzena Memorial da ke Zanzibar. Ya ƙara da cewa, ana shirin gudanar da jana’izarsa a ƙauyen Kizimkazi da ke wani yankin na tsibiri a Zanzibar.
Ameir dai ƙwararre ne kan harkar ilimin noma wanda ya yi rayuwa cikin hali na gama-garin mutane. Ya zama mutum mai nitsuwa na Farko na Tanzaniya a lokacin da matarsa, Shugaba Samia Suluhu a kama aiki a 2021.
Da yake sanar da rasuwarsa, Ndejembi ya mika gaisuwar ta’aziyyarsa ga Shugaba Samia, iyalan marigayin da abokai, yana mai masa addu’ar samun rahama Ubangiji.
Sannan, marigayin ya kasance ba a ganin sa da matar tasa a bainar jama’a, saidai hakan ya kan faru a wasu lokuta a taruka na musamman.
Ya auri Samia ne a shekarar 1978 kafin ga shiga harkar siyasar ƙasa. Sun haifi ‘ya’ya huɗu – uku maza da mace guda a tare. ‘Yarsu, Wanu Hafidh Ameir ita ma ‘yar siyasa ce, wadda kuma ‘yar majalisa ce a majalisar wakilan ƙasar ta Zanzibar.
