
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Dakarun Sojoji a Jihar Borno, sun yi nasara ceto wata yarinya mai kimanin shekaru 11 da aka yi zargin ‘yan ta’adda sun yi garkuwa da ita zuwa jihar da nufin samar da bayanai kan sojoji.
Sojojin Shiyya ta 82 ta Task Force Battalion ne suka samo yarinyar mai suna Aisha Mustapha yayin wani sintiri a yankin Armuda General da ke Ƙaramar Hukumar Gwoza.
Majiyoyin tsaro sun shaida wa Zagazola Makama cewa al’amarin ya faru ne da misalin ƙarfe 1:41 na daren ranar 4 ga Satumba, 2026.
Sun yi zargin cewa, Aisha tana ɗaya daga cikin mutane uku da wasu mutane biyu da ake zargin ‘yan ta’adda ne sun ɗauko su daga ƙauyen Mountain a yankin Saha. Bincike ya nuna cewa, ana zargin ‘yan ta’addar da shirya amfani da mutanen wajen sanya ido kan ayyuka da zirga-zirgar sojojin da aka jibge a yankin Ngoshe.
A cewar majiyoyin, mutanen da aka saton sun yi arangama ne da dakarun yayin sintirin, lamarin da ya angiza Aisha ta sheƙa da gudu ta je wajensu tare da miƙa wuya a gare su. Sauran biyun kuma suka tsere ta yankin ƙauyen. Tuni dai jami’an suka kai yarinyar sashen bayar da kulawa yayin da suke ƙoƙarin damƙa ta ga iyalanta.
Wannan al’amari ya nuna yadda halin tsaro ke cigaba da fuskantar ƙalubale a yankin Gwoza, inda ake zargin ‘yan ƙungiyoyin ta’addanci da ƙoƙarin lalata tunanin fararen hula marasa galihu ciki har da yara domin samar musu da bayanan sirri.
Majiyoyin tsaro sun ce sojojin da ke aiki a yankin suna cigaba da ƙoƙarin bayar da kariya ga rayukan fararen hula da lalata hanyoyin yunƙurin samun bayanai ta hannu mazauna.
