
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Majalisar Wakilai ta sanar da rushe baki ɗaya kwamitocin wucin-gadin da ta kafa domin gudanar da wasu bincike kan muhimman lamuran ƙasa, inda ta umarci mambobinsu da su dakatar da dukkan ayyukan da aka ɗora musu a nan take.
Rahotanni sun bayyana cewa, umarnin ya biyo bayan ƙarewar wa’adin da aka bai wa kwamitocin ne na su kammala bayar da rahotannin ayyukan da aka ba su da miƙa su gare ta bisa sharuɗɗa da al’adar majalisar. Wannan mataki ya fara aiki ne a ranar Juma’a, 28 ga Agusta, 2026.
Kakakin majalisar, Tajudeen Abbas ne ya sanar da wannan umarni a wata sanarwa da Akawonta, Sidi Ibrahim ya sanya wa hannu, kuma aka gabatar wa shugabanni da mambobin kwamitocin da hakan ya shafa.
A cewar sanarwar, ire-iren kwamitocin biyu ne kaɗai aka ƙara wa wa’adi bisa hukuncin Doka ta 18 da Sharaɗi na 5 na Dokokin majalisar, amma mako biyun da aka ba su ya ƙare.
Haka kuma, an umarci shugabannin kwamitocin da su miƙa kundaddakin rahotannin da ake jiran su bayar, takardun aiki da dukkan wasu ababe masu alaƙa da ayyukan da aka ba su ga akawon majalisar. Don haka aka buƙaci mambobin da su bayar da haɗin kai da tabbatar da cikakken biyayya kan al’amarin.
