
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Jam’iyyar PDP a Jihar Kano, ta ce taron siyasar da jam’iyyar APC ta gudanar a ranar Asabar ba ya nufin cin mutunci, barazana ko karya gwiwa ga magoyanta da ke faɗin jihar.
PDP ta bayyana cewa, tana sane da halin matsin tattalin arziƙi da al’umma suke fuskanta a jihar, yayin da bayan shekaru da dama na halin talauci da matsi a lokacin da aka kawo wani tallafi, za a ga ‘yan ƙasa suna halarta domin su amfana da dukkan wani abin da za a bayar, don haka ta ce kada a ɗauki halartar taron siyasa a matsayin amincewa da goyon bayan wata jam’iyyar siyasa.
A sanarwar da Sakataren yaɗa labaranta, Kwamared Ahmed Dauda Lawan ya fitar, PDP ta ce: “Ya kamata kowa ya fahimta, taron siyasa ba zaɓe ba ne.”
A cewarta, a ranar zaɓe za su fito domin yin amfani da damar da dokar ƙasa ta ba su na zaɓar waɗanda suke so da fatan samun adalci daga gare su, saboda haka babu wani taro, rabon kuɗi ko fitar siyasar da za ta yi tasiri kan ikonsu.
Haka kuma, PDP ta bayyana damuwarta kan yadda ake amfani da dukiyar al’umma wajen gudanar sa harkokin jam’iyyar siyasa, tana mai cewa kuɗaɗen gwamnati na al’ummar Kano ne ba na wata jam’iyya ko ƙungiyar siyasa ba.
Sannan, sanarwar ta ce PDP jam’iyyar ‘yan Kano ne. “Mambobinmu suna biyan haraji, ƙwararru ne, ma’aikata, ‘yan kasuwa, mata, matasa da masu ruwa da tsaki ne su a wannan jiha.”
Don haka ta ce akwai buƙatar a riƙa yin adalci da samar da daidaito wajen sarrafa dukiyar al’umma, inda ta ce matuƙar za a riƙa ɗaukar dukiyar jihar ana wadaƙa da ita da sunan tallafa wa harkokin siyasa, wajibi ne gwamnati ta shirya yin bayanin dokar da ta shar’anta yin hakan da tabbatar da cewa babu wani ɗan jiha da aka nuna wa wariya saboda bambancin jam’iyya.
