Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Sanata Abdul’aziz Musa Yar’adua da Hajiya Hafsat sun miƙa makarantar Mariganya Hajiya Dada ga hukumar Zakka da Waƙafi ta Jihar Katsina.
Makarantar da Marigayiya Hajiya Dada ta gina, ana koyar da ilimin addinin Musulunci da na boko. Bayan rasuwarta, makarantar ta koma hannun Sanata Abdulaziz da Hajiya Hafsat, waɗanda daga baya suka yanke shawarar mayar da ita waƙafi ga iyayensu, Marigayi Alhaji Musa Yar’adua da Marigayiya Hajiya Dada, da kuma kawunansu.
Hajiya Hafsat, wadda ta wakilci Sanata Abdulaziz, ta ce sun miƙa makarantar ga hukumar ne domin a ci gaba da kula da ita tare da tabbatar da ɗorewar ayyukan alherin da aka kafa ta a kansu.
Ta kuma bayyana cewa tuni suka fara wasu gyare-gyare a makarantar domin inganta yanayin karatu.
Da yake karɓar waƙafin, shugaban hukumar Zakka da Waƙafi ta Jihar Katsina, Dr. Ahmad Musa Abdullahi, ya yaba wa Sanata Abdulaziz Musa Yar’adua da Hajiya Hafsat Musa Yar’adua bisa wannan gagarumin aikin alheri, yana mai cewa irin wannan mataki na nuna kishin ci gaban ilimi da taimakon al’umma.
Dr. Ahmad ya bayyana cewa waƙafi na daga cikin manyan ayyukan alheri da Musulunci ya ƙarfafa, musamman saboda amfaninsa yana iya ci gaba da kasancewa ga al’umma na tsawon lokaci, yayin da ladan wanda ya kafa waƙafin ke ci gaba da samuwa.
Ya ce waƙafin makaranta ya fi muhimmanci saboda yana haɗa ilimi da sadaka mai gudana, inda ɗalibai ke samun ilimin addini da na zamani, tare da samun tarbiyya da kyawawan ɗabi’u. Ya ƙara da cewa duk wanda ya taimaka wajen ilimantar da ɗalibi, yana da babban rabo a cikin alherin da wannan ilimi zai haifar a rayuwarsa da kuma bayan rayuwarsa.
Shugaban hukumar ya ce wannan waƙafi zai taimaka wajen tabbatar da cewa makarantar ta ci gaba da kasancewa cibiyar ilimi mai amfani ga al’umma, ba tare da manufar waƙafin ta gushe ba.
Ya kuma jaddada cewa hukumar za ta tabbatar da kula da makarantar da kadarorinta bisa ƙa’idojin waƙafi, tare da yin aiki tare da iyalan gidan domin ganin an cimma manufar da aka kafa waƙafin a kanta.
Dr. Ahmad ya kuma yaba wa iyalan gidan Matawalle bisa irin gudummawar da suka daɗe suna bayarwa wajen ayyukan alheri, yana mai addu’ar Allah ya karɓi wannan waƙafi, Ya sanya shi sadaka mai gudana, Ya kuma yawaita ladan waɗanda aka sadaukar da waƙafin domin su.
Shi ma babban sakataren Hukumar, Dr. Abubakar Yusuf, ya bayyana muhimmancin waƙafin, yana mai cewa hukumar tana da tsare-tsare na musamman wajen kula da kadarorin waƙafi da tabbatar da dorewarsu.
Ya ce hukumar za ta yi aiki tare da iyalan gidan wajen ganin makarantar ta samu kulawar da ta dace, tare da tabbatar da cewa manufar waƙafin ta tabbata.
Marigayi Dada itace mahaifiya ga tsohon shugaban ƙasa Marigayi Umaru Musa Yar’adua.
