Daya daga cikin manyan buƙatun wannan zamani shi ne samar da ingantaccen bayani game da addinin Musulunci – Aisha Lemu
Daga AISHA ASAS
Shafin Gimbiya na wanonan makon ya kawo muku wata mace wadda Arewa da Najeriya suke da dalilin tunawa da ita. Mace ce da ta shafe fiye da rabin ƙarni tana aikin ilimi, Da’wah da kuma ƙarfafa mata, duk da yake ba ’yar Najeriya ba ce ta asali, ta zabi Najeriya ta zama gidanta, ta kuma sadaukar da mafi yawan rayuwarta wajen gina abubuwan da har yau ake ci gaba da amfana da su. Ita ce Hajiya Aisha Lemu, wadda ta taka muhimmiyar rawa wajen kafa Islamic Education Trust (IET) a shekarar 1969, sannan ta kasance cikin waɗanda suka kafa Federation of Muslim Women’s Associations in Nigeria (FOMWAN) a shekarar 1985, inda ta zama Amirah ta farko ta ƙasa.
Amma kafin mu shiga cikin tarihin ayyukan da suka sanya sunanta ya yi fice, akwai wata tambaya da ya kamata mu fara da ita: Shin wace ce Hajiya Aisha Lemu? Ta yaya wadda aka haifa a Ingila, ta taso cikin wata al’ada da addini daban, ta kai ga karɓar Musulunci, sannan ta zo Najeriya ta zama malama, marubuciya, jagorar mata kuma ɗaya daga cikin ginshiƙan ilimin Musulunci a ƙasar? Wannan ce tafiyar da Shafin Gimbiya ta wannan makon zai jagorance ku zuwa gare ta. Aisha Asas ce ɗauke da tarihin macen da ta cancanci a kira ta da Gimbiya, Hajiya Aisha Lemu.
Idan kun shirya, zan ce a sha karatu lafiya.
Shin wace ce Hajiya Aisha Lemu?
An haifi Aisha Lemu a Poole, Dorset, a Ingila, a shekarar 1940, da sunan Bridget Aisha Honey. Ta taso ne a cikin Church of England, amma tun tana matashiya ta fara samun wasu tambayoyi game da addinin da ta buɗe ido ta ganta a ciki.
A lokacin da take da shekara 13, ta fara bincike kan wasu addinai, ciki har da Hindu da addinan Gabas, domin tana son ta fahimci abin da ta yi imani da shi, maimakon ta karɓi abu kawai saboda haka aka koya mata. Wannan neman amsa ya ci gaba har zuwa lokacin da ta shiga School of Oriental and African Studies (SOAS) ta Jami’ar Landan, inda ta yi karatu tare da sha’awar tarihin Chana, harshe da al’adunta. A can ne haɗuwarta da wasu Musulmai da kuma littattafan da suka ba ta ta karanta suka buɗe mata wata sabuwar hanya. A shekarar 1961, a lokacin shekararta ta farko a SOAS, ta karɓi Musulunci a Islamic Cultural Centre da ke Landan, sannan ta ɗauki sunan Aisha.
Amma karɓar Musulunci bai sa ta ja birki wajen neman ilimi ba. Maimakon haka, ya ƙara zurfafa sha’awarta ga abin da ta karɓa. Ta shiga ayyukan musulman ɗalibai a SOAS, ta taimaka wajen kafa Islamic Society kuma ta zama sakatariyar farko ta ƙungiyar, sannan ta taimaka wajen kafa Federation of Student Islamic Societies. Wannan mataki na farko yana da muhimmanci wajen fahimtar Aisha Lemu, domin tun kafin ta zo Najeriya ta riga ta fara koyon yadda ake mayar da ilimi zuwa aiki, da kuma yadda ake haɗa mutane a ƙarƙashin manufa guda.
Ko me ya sa Aisha Lemu ta zo Najeriya?
Bayan kammala karatunta a SOAS, Aisha ta samu ƙarin horo a fannin koyar da Ingilishi a matsayin harshen waje, inda ta samu Postgraduate Certificate in Education. A wannan lokacin ne ta ƙara kusantar Sheikh Ahmed Lemu, wanda shi ma yake karatu a Jami’ar Landan kuma yake cikin ayyukan Musulunci. Wannan haɗuwa ta zama wani muhimmin sashe na rayuwarta, domin daga baya zai zama abokin rayuwarta kuma abokin aikinta a fannonin ilimi da Da’wah. A watan Agustan 1966, Aisha ta zo Najeriya, inda ta fara koyarwa a School for Arabic Studies da ke Kano, makarantar da Sheikh Ahmed Lemu ke jagoranta.
Zuwanta Najeriya ba ta kasance da zumar yin ziyarar aiki da za ta dawo daga ita ba. Bayan kusan shekara ɗaya da rabi a Kano, ta koma Sokoto, inda ta zama Principal ta Government Girls’ College. Daga baya, a shekarar 1976, lokacin da aka kafa sabuwar Jihar Neja, ta koma Minna, inda ta zama Principal ta Women Teachers’ College, matsayin da ta riƙe har zuwa 1978. A cikin waɗannan shekaru na koyarwa da shugabanci, Aisha ta fara ganin matsalolin da ke cikin tsarin koyar da Islamic Studies a makarantu, kuma abin da ta gani a aji ya taimaka wajen sauya tunaninta daga kasancewa malamar makaranta kawai zuwa mace mai son ta ga an gyara tsarin ilimin Musulunci gaba ɗaya.
Shin me ta fahimta a koyarwar da ta yi a Islamic Studies?
Lokacin da Aisha ta fara aiki a Najeriya, ta lura cewa koyar da Islamic Studies a wasu makarantu ya fi karkata ga koyar da ɗalibai abin da za su yi, kamar yadda ake yin sallah ko azumi, amma ba a ba su cikakkiyar fahimtar dalilin yin waɗannan abubuwa ko yadda koyarwar Musulunci za ta shafi tunaninsu da halayensu.
Wannan ya ba ta mamaki, musamman ganin cewa ita kanta tafiyarta zuwa Musulunci ta samo asali ne daga tambaya, bincike da neman fahimta. Saboda haka, ta fara ganin cewa ilimin addini ya kamata ya wuce haddace bayanai; ya kamata ya taimaka wa ɗalibi ya fahimci addininsa, ya gina ɗabi’a, sannan ya iya amfani da abin da ya koya wajen gudanar da rayuwarsa. Wannan fahimta ce daga baya ta shiga cikin aikinta na rubuce-rubuce da kuma ƙoƙarinta wajen gyaran manhajar Islamic Studies.
Aisha ta zama memba a Islamic Studies Panel da Nigerian Educational Research Council ta kafa domin duba da sabunta manhajar Islamic Studies a matakai daban-daban na makarantu. Wannan ya ba ta damar yin tasiri ba kawai kan ɗaliban da take koyarwa a ajinta ba, har ma kan tsarin da ake amfani da shi wajen koyar da dubban ɗaliban Najeriya. A nan ne aikinta ya fara samun faɗin da ya wuce makarantar da take shugabanta.
Bari mu koma wata babbar ƙofa a rayuwar Aisha Lemu. Shin ita da Sheikh Ahmed Lemu ne suka kafa Islamic Education Trust, kuma me ya sa suka kafa ta?
A shekarar 1969, Aisha Lemu, Sheikh Ahmed Lemu da Alhaji Sani Ashafa suka kafa Islamic Education Trust, wadda aka kafa a matsayin ƙungiya mai zaman kanta da ta mayar da hankali kan Da’wah, ilimi da jin daɗin al’umma. IET ta samu amincewar gwamnati daga baya, kuma daga ƙaramin tushe ta ci gaba da gina makarantu, wallafe-wallafe, cibiyoyin ilimi da sauran ayyuka. Har zuwa yau, IET tana bayyana waɗannan fannoni uku, wato Da’wah, Education da Human Welfare, a matsayin ginshiƙan aikinta.
Aisha ta taka muhimmiyar rawa wajen ɓangaren ilimi da wallafe-wallafen IET. Ta taimaka wajen samar da kayan koyarwa, littattafan Islamic Studies da kuma hanyoyin da za a sa ilimin addini ya zama mai fahimtar da ɗalibai. Daga baya, a shekarar 1978, ta zama Darakta a IET, inda ta ci gaba da haɗa aikin ilimi da Da’wah da rubuce-rubuce. Wannan cibiyar da suka kafa tare ta zama ɗaya daga cikin manyan abubuwan da suka ɗauki mafi girman ɓangare na rayuwarta.
To, ina rubuce-rubucen Aisha Lemu suka shiga?
Idan muka ce Aisha Lemu malama ce, bai kamata mu bar wannan tambayar ba: Shin me ta rubuta da ya sa har bayan rasuwarta ake ci gaba da ambaton sunanta a duniyar ilimin Musulunci?
Aisha ta kasance marubuciya mai yawan aiki. Ta rubuta littattafai da kayan koyarwa da suka shafi Islamic Studies, mata, Da’wah, tarbiyya, hulɗar addinai da sauran fannoni. Kundin ayyukanta da IET ta adana ya haɗa da Methodology of Primary Islamic Studies, Islam: One God, One Humanity, Women in Da’wah, Revelation and the Scriptures: An Islamic Perspective, Islamic Citizenship and Moral Responsibility da wasu ayyuka da dama. Haka kuma akwai littattafan Islamic Studies na matakan Junior da Senior Secondary da aka danganta da aikinta.
Ba wai yawan littattafan kawai ne abin lura ba. Abin da ya fi muhimmanci shi ne faɗin batutuwan da ta shigar. Ta yi rubutu kan yadda ake koyar da Musulunci, matsayin mata, ɗabi’a, ɗan ƙasa, dangantakar addinai da kuma fahimtar addini. Wasu daga cikin ayyukanta sun kasance littattafan makaranta, wasu takardu ne da aka gabatar a tarurruka, wasu kuma rubuce-rubuce ne da suka kai ga masu karatu a wajen Najeriya. Wannan ya sa gadonta na rubuce-rubuce ya kasance ɗaya daga cikin abubuwan da suka fi tabbatar da cewa aikinta bai tsaya ga lokacin da take raye ba.
Bari mu koma bangaren iyali. Ko Aisha Lemu na da iyali?
Bayan kasancewa malama, marubuciya da jagorar mata, akwai wata Aisha Lemu da ba za a iya fahimtar cikakken tarihinta ba tare da an duba rayuwarta ta ɓangaren ba. Shin Aisha Lemu ta yi aure, kuma wa ya kasance abokin rayuwarta?
A shekarar 1968 ne Aisha ta auri Sheikh Ahmed Lemu, wanda ta fara sani tun lokacin da suke a Jami’ar Landan. Aisha ta zama matarsa ta biyu, kuma daga aurensu aka samu ’ya’ya Nuruddeen da Maryam Lemu, tare da jikoki. Sheikh Ahmed Lemu ya kasance babban malamin Musulunci kuma daga baya ya zama Grand ƙadi na Sharia Court of Appeal ta Jihar Neja lokacin da aka kafa kotun a shekarar 1976. Aisha da shi ba su kasance ma’aurata kawai ba; sun kuma kasance abokan aikin ilimi da Da’wah, musamman wajen kafa IET da gina ayyukan da suka shafi ilimin Musulunci.
Wannan ɓangaren yana ƙara nuna yadda rayuwar Aisha ta kasance haɗe a kowane ɓangare: gida, makaranta, rubutu, Da’wah da ƙungiyoyi duk suna tafiya tare. A cikin wannan rayuwa ta iyali ne ta kuma tarbiyyantar da ’ya’yanta, waɗanda daga baya suka zama sanannu a fannin magana da Da’wah. Saboda haka, lokacin da muke magana kan gadonta, ba wai cibiyoyi da littattafai kaɗai muke magana ba; akwai kuma iyalin da ta bari a baya da kuma mutanen da suka taso ƙarƙashin tasirinta.
Ko ayyukan sun tsaya a iya kafawa da renon IET da FOMWAN kawai?
A’a. Bayan ta shafe shekaru tana aikin ilimi da IET, ta sake buɗe wata sabuwar hanya.
Aisha ta ci gaba da aiki a fannoni daban-daban da suka shafi ilimi, Da’wah da rayuwar al’umma. Bayan wa’adinta na farko a matsayin Amirah ta FOMWAN, ta koma aikin gwamnati kuma ta ci gaba da rubuce-rubuce da halartar tarurruka na ƙasa da ƙasa. Ta yi rubutu a mujallu na cikin gida da na ƙasashen waje, sannan ta gabatar da takardu kan batutuwan Musulunci, Da’wah, ilimi, mata, yara da hulɗar addinai. Wannan yana nuna cewa shugabancin FOMWAN ba ƙarshen aikinta ba ne; wata tasha ce kawai a cikin doguwar tafiyar da ta yi.
Me ya sa ta kafa FOMWAN?
Za mu ci gaba a mako mai zuwa
