Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Jami’an tsaro da hadin gwiwa da ma’aikatar lafiya sun kai samame na bazata a wuraren da ake sayar da yar ƙwamaso a jihar Katsina.
Samamen ya biyo bayan matakai da gwamnatin Katsina ta ɗauka na ƙara tsaurara matakan daƙile safara da sayar da sinadarin ƙwamuso, bayan da jami’an ma’aikatar lafiya tare da jami’an tsaro suka kai samame wasu wuraren da ake zargin ana gudanar da harkar.
Samamen wanda aka gudanar ya shafi wasu wurare daban-dwban a ƙaramar hukumar Mashi da kuma cikin birnin Katsina.
A yayin samamen, jami’an sun kama mutane shida a wani asibitin da ke ƙaramar hukumar Mashi, yayin da aka sake cafke wasu mutum biyu a cikin garin Katsina, bisa zargin hannu wajen safara da sayar da sinadarin ba bisa ƙa’ida ba.
Kwamishinan lafiya na Jihar Katsina Hon Musa Adamu Funtua ne ya kafa wani kwamiti na musamman domin binciken lamarin, wanda kuma shi ne ya jagoranci aikin kai samamen.
Kwamishinan ya bayyana cewa safarar ƙwamuso babban laifi ne, musamman ganin cewa ana samar da sinadarin ne domin taimaka wa yara marasa lafiya da ke fama da tamowa.
Ya ce gwamnatin Jihar na kashe makudan kuɗaɗe wajen inganta harkar lafiya da samar da kayan kula da yara, don haka ba za ta amince wasu mutane su karkatar da kayan kiwon lafiya domin amfanin kansu ba.
Hon.Musa ya yi gargadin cewa, duk wanda aka samu da hannu wajen safara ko sayar da sinadarin ba bisa ƙa’ida ba zai fuskanci hukuncin da ya dace, kamar yadda doka ta yi tanadi.
A nasa bangaren, sakataren kwamitin Dr.Umar Bello Bindawa, ya ce samamen na daga cikin matakan farko da kwamitin ke ɗauka domin gano waɗanda ke safarar ƙwamuso da kuma hanyoyin da ake bi wajen kai sinadarin wuraren da ake sayar da shi.
Ya bayyana cewa, mutanen da aka kama za’a miƙa su ga hukumomin da suka dace domin gudanar da cikakken bincike da ɗaukar matakin doka.
Dr.Bindawa ya kuma yi kira ga masu wannan harkar da su dakatar da ita, yana mai cewa gwamnati za ta cigaba da bibiyar duk wata hanya da ake amfani da ita wajen karkatar da sinadarin daga wuraren da aka tanadar da shi domin amfanin yara.
Samamen ya samu halartar jami’an ma’aikatar lafiya, hukumomin kula da lafiya a matakin farko, jami’an tsaro, da sauran masu ruwa da tsaki a fannin abinci mai gina jiki da kula da lafiya.
