
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A ranar Litinin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi ya halarci taron ƙaddamar da ofishin yaƙin neman zaɓen Seyi Makinde, wanda shi ne jam’iyyar APM ta fitar a matsayin ɗan takararta na shugaban ƙasa na babban zaɓen 2027 da ke tafe.
An gudanar da taron ne a Babban Birnin Tarayya Abuja, inda aka ga Obi da wasu sanannun ‘yan siyasa na APM ciki har da jagoranta na ƙasa kuma Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed.
A wasu bidiyoyi da aka yaɗa a kafafen sada zumunta, an ga tsohon gwamnan na Jihar Anambara tare da Bala Mohammed yayin da magoya baya suka taru domin shaida buɗe ofishin yaƙin neman zaɓen gabanin zaɓukan na 2027.
Da yake jawabi a taron, Bala Mohammed ya gargaɗi jam’iyyun adawa da cewa kada su raina ƙarfin APM da ɗan takarar nata, yana mai cewa ta shiga zaɓen shugaban ƙasar ne domin sauya akalar shugabanci a Nijeriya, inda ya kuma wasa ɗan takarar nasu bisa bayyana ƙwarewarsa ga harkokin siyasa da shugabanci.
Gwamnan Bauchin ya kuma kirayi ‘yan Nijeriya da su ɗauki jam’iyyar da burinta na shugabancin ƙasa da muhimmanci yayin da ake cigaba da gudanar da yaƙin neman zaɓen 2027.
Shi ma ɗan takarar shugaban ƙasar na NDC a nasa kalaman, ya bayyana cewa Seyi Makinde ya cancanci ya shugabanci Nijeriya duba da ƙwarewarsa wajen inganta al’umma da shugabanci na gari. Ya kuma yi kira ga ‘yan Nijeriya da su fito yayin gudanar da zaɓukan 2027 su zaɓi ‘yan takarar da suke so ba tare da hayaniya ba ko nuna gaba a tsakaninsu.
