Ginin Abuja ya rushe bayan FCTA ta rufe shi, ‘yan sanda da jami’an kashe gobara sun fara ceto

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Wani gini ya rushe a yankin Wuse Zone 4 da ke Babban BirninTarayya Abuja, inda tuni aka fara aikin ceto yayin da jami’an bayar da agajin gaggawa suka shiga bincike domin gano ko akwai waɗanda al’amarin ya rutsa da su.

Rahotanni sun nuna cewa, jami’an hukumar kashe gobara ta Abuja suna wajen domin aikin ceto, kuma an jibge motocin agajin gaggawa a yankin. Rundunar ‘yan sandan Abuja ta ce ta samu kiran gaggawa kan al’amarin da misalin ƙarfe 7:45 na yammacin ranar Litinin, 7 ga Satumba 2026.

Kakakin rundunar, SP Josephine Adeh ce ta bayyana hakan a wata sanarwa, inda ta ce rundunar ta tura tawagar jami’ai ƙarƙashin jagorancin mataimakin kwamishinan ‘yan sanda reshen atisaye, ACP Edward Akaniyene da kuma kwamandan yanki na Metro, ACP George Ugomadu zuwa wajen.

Ta bayyana cewa, jami’an hukumomi da dama sun garzaya yankin domin bayar da agaji, waɗanda suka haɗa da na National Emergency Management Agency (NEMA), Federal Road Safety Corps (FRSC), Federal Roads Maintenance Agency (FERMA), Federal Fire Service (FFS), Security Service Department, Federal Capital Territory Administration (FCTA) da wasunsu.

Da fari Reshen Kula da Ci-gaba na FCTA ya rufe gidan da kuma umartar mutanen da suke ciki da su fice daga cikinsa. ‘Yan sandan sun ce bincike ya nuna cewa sashen na hukumar raya birnin tarayyar ya yi wa ginin alama kuma ya rufe shi.

A cewar ‘yan sanda, babu wani rahoton jikkata ko mutuwa kan faruwar al’amarin duk da cewa ana cigaba da gudanar da atisayen bincike da ceto domin gano ko akwai waɗanda al’amarin ya rutsa da su, tana mai cewa ana kuma binciken gano ainihin abin da ya sabbaba iftila’in da matakin damejin da ya yi.

Haka kuma, rundunar ta yi kira ga mazauna da su kwantar da hankali, kula, ƙaurace wa yankin da kuma bai wa jami’an agajin gaggawa haɗin kai domin samun nasara a ayyukansu. Akan haka ne ta shawarci al’umma da su aika mata da rahoton dukkan wani abin zargi ko neman ɗaukin gaggawa ta lambobinta kamar haka: 08032003913 da 08061581938.

By Babaji

Leave a Reply