Gwamnatin Katsina za ta kashe Naira biliyan 828.646 a matsayin kasafin 2027

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamna Dikko Raɗɗa ya gabatar da kasafin kuɗi Naira biliyan 828.646 na shekarar 2027 ga majalisar dokokin Katsina.

Kasafin kuɗin da ya sanya ma suna ‘Building your Future’ ya bayyana cewar zai inganta rayuwar al’umma da tabbatar da kawo cigaba a birni da karkara da ke faɗin jihar.

Gwamnan ya ce kasafin kuɗin shekara 2027 ya ragu da Naira biliyan 69.23.

Haka kuma ya bayyana cewa kasafin kuɗin zai maida hankali akan Ilimi, Noma,Kiwon Lafiya da bunƙasa ƙasa.

Malam Dikko Raɗɗa ya faɗa cewa gwamnatin sa zafi cika alƙawarin da yayi na kai ayyukan cigaba a duk mazauni 361 na jihar.

Gwamna Raɗɗa ya yaba wa kakakin majalisar dokoki da sauran ‘yan majalisar bisa haɗin kai da gudunmawa da ya taimaka wa gwamnatin wajen aiwatar da ayyukan raya ƙasa.

Yayi magana da dama kan aikace aikace da gwamnatin sa ta aiwatar a kasafin ƙarƙashin kasafin kuɗi na shekara 2026.

A jawabinsa, kakakin majalisar dokoki Rt Hon Nasiru Yahaya ya sanar da cewa majalisar dokoki ta gabatar da ƙudirin guda 50 a zaman da tayi a wannan shekara.

Ya yabawa Gwamna Radda bisa aiwatar da ayyukan raya ƙasa ina ya taɓa kowanne ɓangare da ya shafi cigaban jihar.

By ukarofi