Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Shugaban ƙaramar hukumar Funtua, Hon. Abdulmutallab Jibril Sulaiman Goya, ya jagoranci samame na haɗin gwiwar jami’an tsaro zuwa wasu wurare da ake zargin ‘yan bindiga na amfani da su wajen fakewa da kuma kutsawa cikin garin Funtua.
Samamen, wanda aka gudanar ya ƙunshi jami’an sojin ƙasa, da rundunar sojin sama, da ‘yan sanda, da MOPOL, da DSS, da FRSC, da C-Watch, da Vigilante da Civilian JTF, domin daƙile ayyukan masu aikata laifuka tare da ƙarfafa tsaron al’ummar yankin.
Tawagar jami’an tsaron sun ratsa wasu muhimman wurare da suka haɗa da Cibauna, da Unguwar Biri, da Unguwar Sallah,da Unguwar Tanko, da Rahin Dinya da Rigar Alhaji Garba, da kuma wasu yankunan da ake zargin masu aikata laifuka na amfani da su a matsayin hanyoyin shiga da fita.
A yayin gudanar da samamen, jami’an tsaron sun yi arangama da wasu mutane da ake zargin ‘yan bindiga ne, inda aka samu musayar wuta tsakanin ɓangarorin.
Rahotanni sun ce matsin lambar da jami’an tsaro suka yi ya tilasta wa waɗanda ake zargin tserewa, yayin da jami’an suka samu nasarar ƙwato wasu dabbobi tare da kuɓutar da wasu mutane da aka bari a wuraren.
A wani mataki na ƙara inganta tsaro a Funtua da ƙauyukan da ke kewaye da ita, shugaban ƙaramar hukumar ya kuma fara ƙoƙarin neman ƙarin jami’an tsaro na musamman, ciki har da Special Anti-Robbery/Kidnapping Response Team, domin ƙara wa matakan tsaro ƙarfi.
Wannan yunƙuri ya samu karɓuwa daga wasu mazauna Funtua, waɗanda suka yaba da yadda shugaban ƙaramar hukumar ya nuna jajircewa da ƙudurin haɗa kai da hukumomin tsaro wajen tunkarar matsalar rashin tsaro.
Abin da ya faru ya sake jaddada muhimmancin haɗin gwiwa tsakanin shugabannin ƙananan hukumomi, da jami’an tsaro da al’umma, musamman wajen gano hanyoyin da masu aikata laifuka ke amfani da su da kuma hana su samun mafaka a cikin al’umma.
Ana kuma kira ga mazauna Funtua da su ci gaba da bai wa jami’an tsaro ingantattun bayanai kan duk wani motsi ko mutum da ake zargi, domin taimakawa wajen kare rayuka da dukiyoyi.
Yan kwanakin nan ‘yan bindiga sun yiwa garin Funtua Kawanwa inda a kullun suke kai hare hare a unguwannin da suke kewaye da garin.
