Sojoji sun yi ruwan wuta a sansanonin Boko Haram bayan daƙile harin ƙungiyar a Borno

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Dakarun tsaro na Task Force Birget ta 27 ƙarƙashin Shiyya ta 2 na Atisayen Haɗin Kai a Arewa maso Gabashin Nijeriya, sun yi nasarar daƙile wani hari da wasu da ake zargin mayaƙan Boko Haram ne suka yi yunƙurin ƙaddamarwa akan hanyar Buni Gari zuwa Buratai a Ƙaramar Hukumar Biu da ke Jihar Borno.

Sojojin sun yi arangama da ‘yan ta’addan ne a lokacin da suke gudanar da sintiri a yankin, inda suka mayar da martani cikin salon ƙwarewar aiki, lamarin da ya tilasta musu janye daga yankin a watse. Daga bisani an tura ƙarin wasu dakaru, domin bai wa sojojin damar laluba yankin da tabbatar da cewa sun cika aikin daƙile harin.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar Haɗin Kai na riƙo, Kyaftin Mohammed Goni ne ya bayyana haka a wata takarda da ya fitar a ranar Litinin. Ya ce, atisayen ya kuma taimaka wajen ganowa da lalata sansanonin da ‘yan ta’addan suke amfani da su domin fakewa na wucin-gadi da wasu maɓoya.

Ya bayyana cewa, sojojin sun kuma ƙwato ababe kamar haka: babur guda, kekunan hawa, maɗaukin alburusai, alburusai da wasu ababen fashewa.

Goni ya ƙara da cewa, ba a samu jikkata daga cikin dakarun ba, amma wasu motocin sojoji sun lalace sakamakon musayar wuta. Sannan motar kariyar farmaki ta MRAP ta samu matsala bayan hawa kan wani abin fashewa, wanda hakan ya yi sanadiyyar damejin tayoyinta biyu.

Rundunar sojin ta kuma kirayi al’ummar yankin da su kwantar da hankali tare da sanya ido da gaggauta ruwaito dukkan wani abin zargi ga hukumomin da suka dace domin taimakawa aikin shawo kan matsalolin tsaro a yankin da ma ƙasa baki ɗaya.

By Babaji