Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
An yi kira ga gwamnatin jihar Katsina da ta duba yiwuwar horas da ‘Yan jaridar kafafen yaɗa labarai ta samar da masu bayar da horo daga cikin jiha.
Janar Manaja na tashar gidan rediyon Gram FM, Alhaji Bishir Ahmed ya yi wannan kiran a lokacin da ya karɓi baƙuncin shugabannin ƙungiyar tsofaffin ‘yan jarida na jihar Katsina watau NALVEJ da ta kai mai ziyara a ofishinsa da ke gidan rediyon Gram FM a nan Katsina.
Alhaji Bishir Ahmed ya lura cewa a can da, a kan tura ‘yan jarida zuwa ko Ikko ko Kaduna ko Jos domin samun horo.
Ya ce akwai buƙatar yin haɗin gwiwa da ƙungiyar tsofaffin ‘yan jarida domin su bayar da horo a gidan rediyon jihar Katsina da gidan talbijin na jiha, kai har ma da ma’aikatar yaɗa labarai ta jihar Katsina.
Bishir Ahmed ya gode wa Slshugabannin ƙungiyar tsofaffin ‘yan jarida da suka samu damar kawo ziyara a ofishinsa.
Tun farko da yake jawabinsa, shugaban ƙungiyar tsofaffin ‘yan jarida, Alhaji Mansir Lawal Kaware ya zayyana ayyukan da ƙungiyar ta sanya a gaba a Katsina.
Alhaji Mansir Lawal Kaware ya buƙaci goyon baya na shugabannin kafafen yaɗa labarai domin a inganta aikin jarida don cigaban jihar Katsina da ma ƙasa baki ɗaya.
