Gwamnan Kano ya umarci a yi bincike da gaggauta kamo makasan mai sharhin siyasa Ɗan Shagamu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi alla-wadai da kisan ɗan Soshiyal Mediya kuma mai sharhi kan harkokin siyasa, Ibrahim Khalil da aka fi sani da Ɗan Shagamu.

Haka kuma gwamnan ya bayar da umarni ga hukumomin tsaro da su gaggauta farauto masu hannu a laifin, yana mai bayyana kisan a matsayin abin firgitarwa wanda ba za a lamunta ba, sannan ya bayyana kaɗuwarsa kan abin da ya haddasa aukuwar lamarin.

Wannan na ƙunshe ne a wata takarda da Kakakin gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a ranar Laraba. Gwamna Abba ya kuma buƙaci a gudanar da bincike mai zurfi kan al’amarin domin tabbatar da kamo dukkan waɗanda suke da hannu a ciki tare da hukunta su bisa tanadin doka.

Kazalika, Abba Kabir ya miƙa gaisuwar ta’aziyyarsa ga iyalai, abokai da abokan aikin marigayin, yana mai addu’ar Allah ya jiƙan sa ya kuma gafarta masa kurakuransa.

Ya kuma kirayi al’ummar Kano da su kwantar da hankali tare da kauce wa ɗaukar doka a hannunsu, yana mai tabbatar musu da cewa gwamnatin za ta cigaba da aiki tare da hukumomin tsaro wajen bayar da kariya ga rayuka da dukiyoyinsu a sassan jihar.

By Babaji

Leave a Reply