Majalisar zartarwar jihar Katsina ta amince da ware Naira miliyan 500 a matsayin kuɗin da gwamnatin jihar za ta bayar a matsayin gudummawar haɗin gwiwa wajen sayen kayayyakin abinci mai gina jiki na shekarar 2026.
Matakin na daga cikin ƙoƙarin gwamnatin jihar na yaƙi da matsananciyar tamowa da ke addabar yara a sassa daban-daban na jihar.
Kwamishinan Lafiya, Hon. Musa Adamu, ya bayyana cewa wannan tallafi zai taimaka wajen ci gaba da samar da muhimman kayayyakin abinci mai gina jiki ga yaran da ke fama da matsananciyar tamowa, tare da ƙarfafa matakan da jihar ke ɗauka wajen magance matsalar.
An cimma wannan matsaya ne cikin manyan shawarwarin da aka amince da su a taron majalisar zartarwar jihar Katsina karo na 15, wanda Gwamna Raɗɗa ya jagoranta.
Baya ga harkar lafiya, Mai bai wa gwamna shawara na musamman kan bunƙasa kasuwanni, Mustapha Bala Batsari, ya bayyana cewa majalisar ta amince da zamanantar da wasu zaɓaɓɓun kasuwanni a shiyyoyin sanatan jihar guda uku, ciki har da kasuwannin Dandume, Daura, Mashi da Jibia.
Bala ya ce zamanantar da kasuwannin na daga cikin ƙoƙarin gwamnatin Raɗɗa na inganta kayayyakin more rayuwa na kasuwanci da kuma ƙarfafa jin daɗin rayuwar al’umma ta fuskar tattalin arziki da zamantakewa.
Shi ma kwamishinan yaɗa labarai da al’adu, Dr. Salisu Bala Zango, ya bayyana cewa majalisar ta amince da sayen buhunan hatsi guda 95,000 domin rabawa marasa galihu da masu fama da ƙalubale a faɗin jihar.
Ya ce wannan mataki na daga cikin hanyoyin da gwamnatin Raɗɗa ke amfani da su wajen rage wa al’umma raɗaɗin matsin tattalin arzikin da ake ciki tare da ba da tallafin kai tsaye ga gidajen da ke buƙata.
Zango ya ƙara da cewa majalisar ta amince da saye da raba kayan abinci tare da bayar da tallafin kuɗi ga masu rauni, musamman marayu, zawarawa, mutanen da ke da buƙatu na musamman da sauran marasa galihu.
A cewarsa, majalisar ta kuma amince da gyaran masallatan Jumu’a guda 81 a cikin ƙananan hukumomi 34 na Jihar Katsina.
Ya bayyana cewa wannan mataki na da nufin inganta da kula da kayayyakin more rayuwa na addini, daɗa bunƙasa koyarwar Musulunci da kuma ƙarfafa haɗin kan al’umma.
Dangane da bunƙasa matasa kuwa, majalisar ta amince da kafa Ƙungiyar Model United Nations ta Jihar Katsina (MUNDO), a matsayin wani shiri da gwamnatin jihar za ta jagoranta tare da tallafin abokan hulɗar ci gaba.
