Champions League: Barcelona, PSG, Arsenal da Liverpool sun yi nasara a wasannin farko

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A ranar Laraba ƙungiyoyin Barcelona, PSG, Liverpool da Arsenal suka yi nasara a wasannin farko na gasar Zakarun Nahiyar Turai (UEFA Champions League) na 2026/27 a jimillar wasanni shida da aka buga a sassan yankin.

Daren buɗe gasar na biyu ya samar da ƙwallaye 19 a wasannin da ƙungiyoyi daban-daban suka fafata. Barcelona ta lallasa Feyenoord ta ƙasar Holland da ci 5 da 1, yayin da masu riƙe da kofin, Paris Saint-Germain ta fara da salo mai ban ƙaye da ci 6 da 1 akan Slovan Bratislava.

Ita kuwa Liverpool mai kofin guda shida a tarihinta, ta doke Atletico Madrid da ci 2 da 1 a lokacin da ta farfaɗo a filin wasan na Anfield yayin da Zakaran Premier League Arsenal ya doke SC Napoli a birnin Naples.

Sporting CP kuwa, ta casa Galatasaray ta su Victor Osimhen ne da ci 3 da 1, yayin da VfB Stuttgart ta Jamus ta doke Vikings FK da ta shiga gasar a karon farko da ci 3 da 1.

Ga sakamakon na Laraba kamar haka:
Barcelona 5-1 Feyenoord

VfB Stuttgart 3-1 Viking FK

Liverpool 2-1 Atletico Madrid

Paris Saint-Germain 6-1 Slovan Bratislava

Sporting CP 3-1 Galatasaray

Napoli 0-1 Arsenal

Za a cigaba da fafatawa a rukunin a yau Alhamis inda Manchester United za ta karɓi baƙuncin Sabah, Bayern Munich da Bodø/Glimt, Fenerbahce za ta kara da Roma sai Como ta koci Cecs Fabregas da RB Leipzig.

By Babaji