Gwamna Raɗɗa ya aike da tawagar manyan jami’an tsaro Funtua domin ƙarfafa tsaro

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya aike da wata tawagar manyan jami’an tsaro zuwa Funtua domin duba tare da sake tsara yanayin tsaro a ƙananan hukumomin Funtua, Faskari, Sabuwa, Ɗandume da Bakori.

Tawagar ta ƙunshi kwamishinan harkokin cikin gida da tsaro , kwamishinan ’yan sandan jihar, kwamandan Birged, daraktan hukumar tsaro ta ƙasa (DSS) da kwamandan hukumar tsaro da kare fararen hula ta ƙasa (NSCDC) na jihar.

Ana sa ran tawagar za ta gana da masu ruwa da tsaki kan harkokin tsaro daga ƙananan hukumomin biyar, domin tantance matsalolin tsaro da ake fuskanta a halin yanzu tare da samar da ingantaccen tsarin haɗin gwiwa wajen yaƙi da matsalar a tsakanin al’ummomin da abin ya shafa.

Ƙananan hukumomin sun haɗa da Faskari,Dandume, Sabuwa, Ƙankara da Funtua.

Kafin wannan mataki da Gwamna Raɗɗa ya nemi gwamnatin tarayya ta aike da ƙarin sojoji a Funtua domin dawo da tsaro a garin.

By ukarofi

Leave a Reply