Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Ɗan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party, PDP, na mazabar Zamfara ta tsakiya a majalisar dattawa, Alhaji Sanusi Bala Gusau, ya yi Allah wadai da harin ‘yan bindiga na baya bayan nan a ƙaramar hukumar Bungudu, sannan ya yi alƙawarin bai wa tsaro fifiko idan aka zaɓe shi.
A cikin sakon ta’aziyyar da ya aika wa mutanen Bungudu ranar Lahadi, Gusau ya bayyana kisan a matsayin abin baƙin ciki da zafi, inda ya ce yadda talauci da wahala suka bazu cikin al’umma ya sa siyasa ta zama ta biyu, domin yanzu rayuwa ce ta farko.
“Mutane sun waye yanzu. Talauci ba na siyasa ba ne, domin yanzu kowa yana cikin wahala, in ji shi. “Idan Allah ya ba mu dama, za mu yi duk abin da ya dace domin kawo ƙarshen matsalar tsaro da ke azabtar da mutanenmu.”
Gusau, wanda ke da sarautar Sarkin Dawaki mai tuta a masarautar Gusau, ya miƙa jaje ga iyalai da suka rasa ‘yan uwansu a harin, da kuma waɗanda ‘yan bindiga ke riƙe da ‘yan uwansu.
Ya yi addu’ar Allah maɗaukaki ya kuɓutar da waɗanda aka yi garkuwa da su, kuma ya bai wa Jihar Zamfara zaman lafiya mai ɗorewa.
A cewarsa, matsalar rashin tsaro a Zamfara ta zarce siyasar jam’iyya, kuma tana buƙatar gaggawar ɗauki tare da haɗin gwiwar gwamnati, masarautu, da shugabannin al’umma.
Ya ƙara da cewa ba za a samu ci gaba na gaskiya a jihar ba har sai mutane suna iya noma, kasuwanci, da zirga-zirga ba tare da tsoro ba.
Gusau ya yi kira ga ‘yan ƙasa da su ci gaba da zama tare da goyon bayan dukkan ƙoƙarin da ake yi domin dawo da zaman lafiya.
Sannan ya buƙaci gwamnatin tarayya da ta jihar da su ƙara tura kayan aiki da jami’an tsaro domin kare al’ummomin da ke cikin hatsari a faɗin jihar.
