Babbar Kotun Kebbi ta tura wasu mata gidan yari bisa taimaka wa ‘yan ta’adda

Spread the love

Daga MUHAMMAD SADISU ABUBAKAR, Birnin Kebbi

Wata babban kotun Jihar Kebbi da ke zamanta a Birnin Kebbi, ta yanke ma wasu mata guda uku ɗaurin shekara 14 kowanensu a gidan yari, bisa dalilin haɗa kai da taimakawa ‘yan ta’adda da kuma kasancewa cikin ƙungiyar ‘yan ta’adda.

Amma kotun ta sallami, kuma ta wanke wadda ake tuhuma ta farko dangane da duk laifuffukan da aka gabatar a kan ta.

Da yake yanke hukuncin, Justice Hassan Shehu Kuwwa, yayi amanna cewar ɓangaren gabatar da ƙara ya sauke nauyin da ke kafaɗarsa na tabbatar da laifuffukan a kan waɗanda ake tuhuma, ta biyu da ta uku da ta huɗu, amma ya kasa tabbatar da cewar wadda ake zargi ta farko, Aisha Abubakar, na da laifi.

Su dai waɗanda ake tuhumar, Aisha Abubakar da Jamila Sule da Ramatu Habibu da Zara’u Abdulkarim, an gurfanardasu gaban kotu ne a kan zargi guda uku na haɗa-kai a aikata laifi wanda ya saɓa ma sashi (60)1, da taimakama ta’addanci wanda ya saɓa ma sashi na 48, da kuma kasancewa cikin gungun ‘yan ta’adda, wanda ya saɓa ma sashi na 292 na dokar Penal Code ta Jihar Kebbi, 2021.

Mai gabatar da ƙara, ya yi zargin cewar a ranar 14 ga watan Disamba 2023, a dajin Sabon Gari Hills, dake ƙaramar hukumar Shanga, waɗanda ake tuhumar, sun taimakama ‘yan ta’adda ta hanyar kai masu tabar wiwi da kayayyakin abinci da kuma abin sha.

Domin tabbatar da tuhumar, ɓangaren gabatar da ƙara wanda Barrister M. Sebastian Antak na ma’aikatar shari’a ta Jihar Kebbi, ya jagoranta, ya kira shaidu huɗu, suka bada shaida gaban kotu, sannan kuma ya gabatar da takardun rubuce-rubuce guda takwas a matsayin shaidar nazari (exhibit).

Takardun sun haɗa da jawabai da waɗanda ake tuhumar sukayi a harshen turanci, waɗanda aka fassara zuwa luggar Hausa, kuma kotun ta karɓesu a matsayin shaida.

Justice Kuwwa yace, bayan yayi nazari mai zurfi dangane da duk shaidar dake gaban kotu, ya amince cewar bangaren gabatar da ƙara ya kasa tabbatar da laifuffukan da ake tuhumar wadda ake zargi ta farko, Aisha Abubakar.

Saboda haka, yace ba ta da laifi, kuma ya sallameta, sannan kuma ya wanketa, ya bada umarnin a sake ta nan take, kada a ci gaba da tsareta indai ba a kan wani abu bane na doka.

Sai dai, kotun ta samu sauran waɗanda ake tuhumar ta biyu Jamila Sule, da ta uku Ramatu Habibu, da kuma ta hudu Zara’u Abdulkarim, da duk laifuffukan da aka gabatar ma kotu a kan su, kuma ta tabbatar da dokar ta kama su da laifi.

A jawabin neman jin-ƙai daya gabatar, lauya mai kariya gare su, Barrister R. M. Mayalo, na majalisar lauyoyi ta Najeriya masu bada agajin kariya a Kotu, (Legal Aid Council of Nigeria), ya buƙaci kotun ta tausaya ma matan.

Mayalo yace yana roƙon alƙali mai daraja, da ya dubi halin da waɗanda aka samu da laifi, ta uku da ta huɗu, waɗanda suke cikin kuruciyarsu, sannan kuma suna da ƙananan yara da suke reno, sannan kuma sun rigaya sun zauna gidan waƙafi fiye da shekara biyu da rabi, suna jiran kammala shari’a.

Da yake yanke hukunci, alƙalin ya ce, kotun ta yi la’akari da irin nauyin laifuffukan da aka tuhumesu da su, da kuma tsawon lokacin da suka yi a hannun hukuma.

Justice Kuwwa yace ya saurari roƙon da aka yi na yi masu afuwa, sannan kuma da halin da masu laifin ke ciki, tare da nauyin laifuffukan da suka aikata, waɗanda sun shafi rayuka da dukiyoyin al’ummar Jihar Kebbi.

“Yace bisa tanaje-tanajen dokar laifuffuka ta Jihar Kebbi, 2021, dangane da yanke hukunci da kuma bin diddiƙi, sannan kuma da tsawon lokacin da suka yi a gidan yari, za’a cire yawan shekarun da suka yi a gidan-kaso, suna jiran kammala shari’a, daga adadin shekarun da aka ɗibar masu a yanzu na zamansu fursuna.

Saboda haka, Justice Kuwwa yace, tuhuma ta farko, an ɗaure kowanensu shekara ɗaya gidan yari.

Tuhuma ta biyu, an ɗaure kowanensu shekara ɗaya gidan-kaso da kuma taran kudi naira 100,000, wadda kuma ta kasa biya, za ta kara wata ɗaya ɗaure.

Tuhuma ta uku, an ɗaure kowanensu shekara 14 a gidan-kaso.

Alƙalin ya bada umarnin cewar, duk shekarun ɗaurin da aka yi masu, za su gudana ne kafaɗa da kafaɗa.

By ukarofi

Leave a Reply