An yi garkuwa da babban alƙali a Jihar Kebbi

Spread the love

Daga JAMIL GULMA a Kebbi

An wayi garin Lahadi cike da ruɗani a garin Bunza da kuma Jihar Kebbi bayan da waɗansu mutane suka yi garkuwa da ɗaya daga cikin manyan Joji-jojin jihar Kebbi Honarabul Yakubu Hassan Bunza a gidan sa da ke garin Bunza.

Malam Ahmed Abdullahi Bunza wani makusancin Jojin ya bayyanawa waƙilin jaridar Blueprint Manhaja ta wayar tarho da cewa jiya da misalin ƙarfe goma sha biyu na dare ne bayan ya dawo daga Sokoto ne waɗansu mutane kan babura biyar ɗauke da makamai suka tarye shi a ƙofar gidan sa da ke kan hanyar Zogirma suka yi gaba da shi.

Ya bayyana cewa ana sa ran masu garkuwa da mutanen sun daɗe suna bibiyar sa ne sai wannan lokacin suka sami nasarar sace shi.

Ya ƙara da cewa, har ya zuwa yanzu dai ba su kira ba ballantana a sami wata makama ba sai dai jami’an tsaro suna nan suna iya ƙoƙarin su na bibiyar sawun ɓarayin.

Ya nuna sakacin hukuma dangane da rashin bai wa masu irin wannan muƙaman jami’an tsaro don ba su kariya saboda suna daga cikin mutanen da ke aiki mai hatsarin gaske musamman a irin wannan yanayin.

By Babaji

Leave a Reply