
Shugaba Bola Tinubu ya yi kira ga likitoci da sauran ƙwararrun ma’aikatan lafiya na Nij reriya da ke zaune a ƙasashen waje su dawo gida domin ba da gudunmawa wajen bunƙasa harkokin lafiya da ci gaban ƙasa.
Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a yayin da ya karɓi baƙuncin mambobin Ƙungiyar Likitocin Najeriya mazauna ƙasashen waje, ƙarƙashin jagorancin babbar daraktar hukumar ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje (NiDCOM), Abike Dabiri-Erewa, a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Shugaban ƙasar ya ce shi ma ya taɓa karatu da aiki a Amurka kafin ya dawo Najeriya, yana mai jaddada cewa “babu inda ya kai gida.” Ya buƙaci mahalartan su ƙarfafa sauran ƙwararrun ma’aikatan lafiya da ke ƙasashen waje su dawo domin taimakawa wajen gina ƙasa.
Tinubu ya kuma tabbatar da cewa gwamnatinsa na ci gaba da yaƙi da talauci tare da inganta walwalar al’umma, yana mai yabawa gudunmawar likitocin ‘yan Najeriya na ƙasashen waje wajen ƙarfafa tsarin kiwon lafiya na ƙasar.
Ziyarar ta zo ne daidai lokacin bikin Ranar ‘Yan Najeriya Mazauna Ƙasashen Waje ta 2026, wanda NiDCOM ta shirya domin tattauna hanyoyin amfani da ƙwarewar likitocin Najeriya da ke ƙetare wajen inganta tsarin kiwon lafiya da ci gaban ƙasa.
